♦Meyasa Nafadi Jarrabawar JAMB?
Kashi Na 1
(anbuga a 05-02-2019 an Sabunta a, 02-06-2021)
•Shi Ban iya Computer Bane?
•Shin Ban iya Karatun Bane?
•Mecece Matsalar?
Amsar Wannan Tambayar Tana Kunshe Ne a Abunda ka iya Hararowa Kai da kanka kokuma Wani wanda Yafahimci Hakikanin Matsalar ka!
Kungiyar Asof. Tadamu Matukar Damuwa Wajen Ganin Yawan Daliban Arewa Dasuke Faduwa
Jarrabawar JAMB,
Dayawa Daga Cikin Su da Asof. Ta zanta Dasu wasu Sunyi Jarrabawar so Biyu wasu so uku wani Ma da Asof. Ta Tattauna Dashi So biyar Yayi JAMB beci Ba!( Allah yakiyaye)
a ina Matsalar Take?
1•JAMB ba Jarrabawa ba;
Wannan Wani Kallo ne Da Dalibai Sukeyi Wa JAMB Wato Suna ganin cewar Tunda Jarrabawar a Computer Akeyin Ta,
kuma obj Ce Wato Zabi ka-tiqa, Basai Sunyi karatu ba Ai JAMB Sa'a Ce!
Matakin Farko Kenan Dayake Kada Daliban Mu Na Arewa.
•Hanyar Gyara Matsalar Farko;
Ya Dan Uwa Kasani Cewa Jarrabawar JAMB Kamar kowacce Jarrabawa Ce Malamai ne a Kowanne Bangare Suke Shirya Tambayoyin, kuma Computer tana iya Fahimtar Cewa ka Amsa Tambaya Dai Dai ko Akasin Hakan,
Kamar Yanda Ka'amince Cewa Computer tana iya Ganowa idan kudin wayar ka Yakare ko Data,
Shin kayi Tunani wayar ka Zatayi Kira idan babu Kudi?
Computer Datake Lura da Wannan Bangare Tagano baka da Kudi Kamar Yanda computer take iya Gano Amsar ka shin Dai Dai ce Ko A'a a Lokacin Dakake Amsa Tambayoyin JAMB.
Yazama Wajibi Muyi karatu Kamar Yanda Mukeyi a kan kowacce Jarrabawa, Bari Made muyi Karatun Sama da Irin Wanda Mukeyi a Sauran Jarrrabawa
Sbd Kamar Yanda kuka Sani JAMB So Daya Akeyin ta a Shekara.
•Shawarwari Akan Wannan Batu:
1•>Pass Questions Paper
2•>JAMB Syllabus and Objectives
3•> Littafan Karatu
4•>Lokaci Na Musamman
5•>Bibiyar Malamai
1•Idan Muka Duba Abu Nafarko Zamuga Tabbas Bekamata kashiga Dakin Jarrabawar JAMB ba Batare da Kasan Tsari da yanayin Yanda Ake Shirya Tambayoyin ba, Mallakar Pass Q Zai Taimaka Maka Matuka Wajen Fahimtar Abubuwa (ASOF. Ta turo Past Q Din a Group dinta Na JAMB a WhatsApp)
2•Syllabus kuwa Dashine Zaka San shin Me zaka Karanta?
Misali Kai Dalibi Ne da Zakayi Chemistry Ko Economic shin Me zaka karanta Tunda Chemistry Yanada Fadi Sosai, Idan kasamu syllabus Tabbas zaka San inda Yakamata kakaranta (ASOF. Ta turo Past Q Din a Group dinta Na JAMB a WhatsApp)
3•Littafin Karatu Shine Jigon Kowanne karatu idan baka da Littafin karatu Tamkar Manomi NE Dayaje Gona babu Fartanya, Akwai Littafan da JAMB Dakanta Take bada Shawarwarin Akalla Mutum Ya Sayi Daya a Kowanne subject dazeyi a JAMB (idan Babu Hali ko browsing Dalibi yadinga yi)
4•Yazama wajibi ka Kebance Lokaci Na Musamman Domin Yin karatu Cikin Nutsuwa Hakan Zai baka Damar Fahimtar Komai
5•Ba Wai ko Yaushe Kai Kadai zakake karatu ba Komun Sanin ka da ilimin ka baka Kai kowa ba, Yakama ta Kadinga Bibiyar Malamai ko Abokan Karatun ka Domin kakara Fahimtar Abubuwa Dayawa(karawa Juna Sani)
Kungiyar Arewa Students Orientation Forum(ASOF)
Tadaura Damarar Samar Da Sauyi Sosai a Wannan Shekarar Ta Bangaren Samun Dalibai Masu Yawa dazasu Ci Jarrabawar da Taimakon Allah.
Zamu Cigaba insha Allah a Darasi Nabiyu Zakuji Sauran Bayanai.
@ASOF2021
WHATSAPP
08038485677