MISALAI DA BAMBANCEN-BAMBANCEN KARE-KAREN HARSHEN HAUSA



Rubutunka Tunaninka

MISALAI DA BAMBANCEN-BAMBANCEN KARE-KAREN HARSHEN HAUSA

Da farko, bari in ƙara tuna mana tsarin yadda Hausar take ta haka za mu iya bambance yadda Hausar kowanne ɓangare;
(1) *HAUSAR GABAS:* su ne; Kananci, Bausanci, Zazzaganci, Ƙudduranci/Gudduranci, HaÉ—ejanci 

(2) *HAUSAR YAMMA:* su ne; Sakkwatanci, Kabanci, Gobiranci, Zamfaranci

(3) *HAUSAR AREWA;* wadda ta haÉ—a da: Dauranci, Gumalanci, Katsinanci, Damagaranci Da sauransu.

*KARIN HARSHE DA DAIDAITACCIYAR HAUSA*
Yanzu bari mu dubi misalan yadda wasu kare-karen harshe suke da kuma yadda suke a daidaitacciyar Hausa:

*"TS"*
Kare-karen Yamma D/H
tcimi tsimi
hatci hatsi
tcere tsere
watce watse
rantcatce rantsattse
(a lura wajen furta "ts" sai su furta "tc")

*MUSAYAR ƘWAYOYIN SAUTI*
A nan ana nufin yadda wasu suke amfani da wata ƙwayar sauti madadin wata.
Sautin "h" maimakon "f"
Yamma D/H
hwata fata
ƙahwa ƙafa
sassahe sassafe
hili fili
laihi laifi

A dangin Dauranci kuwa "sh" mai wasalin "i" ko "e" ita ke zama "h". Mai wasalin "a" kuwa tana zama "hy" ne, kamar haka:
Dangin Dauranci D/H
hirwa shirwa
farahi farashi
hekara shekara
tahe tashe

hyakka shakka
hyayi shayi
hya'ani sha'ani
hyahyanci shashanci

Bayan haka, dangin Dauranci, wani lokaci ma har da wasu kare-karenn yamma, sukan É—auri "I" maimakon "r", kamar haka:

Dangin Dauranci D/H
galgaÉ—i gargaÉ—i
halbi harbi
kalkashi karkashi
malka marka
walwala warwara
zalÉ“e zarÉ“e 

*A Bausanci, "c" mai wasalin "i" tana zama "sh", kamar haka:
Bausanci D/H
shiki ciki
shitta citta
shigiya cigiya
binshike bincike
dagashi dagaci
takaishi takaici

Idan muka dan bi waɗannan misalan za mu ga yadda wasu suke furta wasu kalmomi, ke nan idan marubuci yana son ya bambace wa mai karatu, tauraro Basakkwace ko Bakano ko Bakatsine ko Badamagare ko Bagumule ko Badauri ne yana buƙatar furucin da ya shafi karin harshensa, ba kawai ya ce tauraro kaza Basakkwace ne amma Hausarsa ta Gumel ko ta Katsina da sauransu.

*ƘA'IDOJIN RUBUTUN HAUSA*

*Ci gaba/Cigaba*

Ta farko ta zo ne a matsayin aiki, wato *ci gaba da yin wani abu* don haka a rabe take zuwa. Misali: 

*Zo ka 'ci gaba' da yin wannan aikin.*

Ta biyu kuma a matsayin suna take, don haka a rabe take zuwa, misali:
*Lallai na yarda an samu 'cigaba' a darasin nan."*

*Farinciki/farin ciki*
*Farinciki* a nan suna ne, misali: 
*Kodayaushe yana cikin farinciki da annashuwa.*
*Farin ciki* wannan kuwa, sifa ce ko aiki
*Za ka yi farin ciki idan ka samu.*
*ÆŠaliban suna ta farin ciki da samun nasarar.*

*Baƙinciki/Baƙin ciki*
Haka su ma waÉ—annan hukuncinsu É—aya da na *farinciki/farin ciki*

Shikenan
*Shikenan;* na nufin an kammala abu, ko abu ya kammata. Misali:
1- *Ai shikenan tun da ka siyar.*
2- *Shikenan je kawai.*
3- *Ai shikenan, sai mu tafi ko." 4- *Ƙurunkus, shikenan.*

*Shi kenan*
Kalmar *shi* wakilin suna ne na mutum namiji, misali:
1- *Shi kenan kullum cikin ciye-ciye.*

2- *Wai har yanzu rigima yake?" "E mana, shi kenan cikin rigima a kullum."*

*Tambayoyi*
Ƙofa a buɗe take ga masu son yi tambayoyi, domin ta haka za a fi fahimtar shirin.

Mu haÉ—u a wani satin, na gode
Kabiru Yusuf Fagge

Manazarta:
Bunza, A.M. (2002) "Rubutun Hausa: Yadda Yake Da Yadda Ake Yin Sa. Don Masu Koyo Da Koyarwa." Ibrash Islamic Publications Centre LTD., Surulere, Lagos.
Indabawa, I.M da Fagge, K.Y (2014) Dabarun Rubuta Kagaggun Labarai." Gimbiya Publishers, Fagge, Kano.
Zarruk, R.M. da wasu (2010) "Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa. Don Kananun Makarantun Sakandire." Ibadan Press Plc, Ibadan Nigeria.
Yahaya, I.Y. () "Darussan Hausa: Don Manyan Makarantun Sakandare." University Press, Plc.
Post a Comment (0)