RUBUTACCIYAR WAƘAR BABA INA ZA KA NE



BABA INA ZAKA NE

Rububutacciyar waƙar Baba Ina Za Ka Ne daga fasihin mawaƙi Aminu Ladan Abubakar Alan waƙa. 



Baba ina zaka ne 
Mulki an yi an gama 
Yanzu gida zani ni 
In zauna da 'yan uwa. 

Baba ina zaka ne 
Mulki ka yi ka gama 
Yanzu gida zani na 
In zauna da 'yan uwa. 

Na tuna sanda munka kammala mulki a tenuwa
Mukai handi-oba fuskoki babu damuwa
Babu kwatankwacinmu tsaf a jiki namu nutsuwa
Ko ɗis ko ƙiris zukatanmu fa babu damuwa.

Baba ina zaka ne 
Mulki an yi an gama 
Yanzu gida zani 
In zauna da 'yan uwa. 

Loton nan idan ka ganni fa zan baka sha'awa
Komai na acan-acan sutura ta gwanin ƙawa
Ga kadara a ko'ina filaye ko da yawa
Sannan ga gida na kwancina ya yi unguwa.

Ga tsirrai cikin furanni sa ba ka sha'awa
Sannan ga ma'aikatan hidima sun yi min yawa
Ga mai ban-ruwa na shuka ga mai dahuwa
Ga me wanke sutura ga me tuƙa tsohuwa.

Sannan ga direba nawa na kaina a nutsuwa
Sannan ga direba me kai yara school kuwa
Sannan ga direba me kai mata fa unguwa
Motoci kala-kala har da ta haura tsakuwa.

Kowane mako uku me fenti yana zuwa
Ya sabunta fente-fente a waje da ƙoƙuwa
Sannan masu ɗamara na bina da zaƙuwa
Ko tsuntsu ya wulƙita zai baƙunci mutuwa.

Sannan shekaru fa sun ja tsufa yana zuwa
Boko ya hanani auren wuri don ɗimuwa
'Yan yara dagwai-dagwai babu guda na garkuwa
Ga saƙo na mutuwa tsufa ya yi garkuwa.

Ban kula ba da dukka esfansib ya yi min yawa
Albashin ma'aikata da yawa ya yi min yawa
Sannan ga kuɗin sukul fis yara yana yawa
Na manta a yanzu income kuma ba sa zuwa.

Sannu akan hankali fa tunani yana yawa
Sannan ga yawan lalurori sun yi min yawa
Sanda na je gwajin jini aka ce ya hauhawa
Ga tari ina ta yi sannu yana ta daɗuwa.

Nai maza na yi firgigit na dawo da nutsuwa
Nai farga irin ta fargar-jaji da makuwa
Ɗan sauran kuɗin da kadarori sun yi raguwa
Sai na nemi yin sana'a na kama kasuwa.

Duk sana'ar da na yi ba riba ba batun uwa
In da na sa ƙafa duka ba sa aya-beguwa
Kai kafin in ankara komai nau ya bi ruwa
Kwanci-a-tashi masu aikin ma ba sa zuwa.

Sannu a hankali furanni sai bubbushewa
Ga fentin jikin gidana na ɓanɓarowa
Gidan ya yi min yawa hidima tai akwai yawa
Na biɗi okshoniya nai gwanjon abubuwa.

An ce malu-wal-banunu a duniya yake ƙawa
Ga 'ya'ya da dukiya yau sun zam baƙar ƙawa
Cuta ci take kuɗi kullum na rage yawa
Har na fara sai da kadarorin nan fa me yawa.

Raina ya ɗugunzuma in na je ni wucewa 
Zunɗe na kawai ake wasu ma na mini shewa 
Gani ina ta tafiya ba comboy na garkuwa 
Sannan banu jiniya taken gani nan zuwa. 

Da in na wuce a titi ka ga ɗaga hannuwa 
Ba me damuwa da amsawa ta da kulawa 
Yanzu ko babu me kulawa wane yake zuwa 
Sai ma in an kula gane wa ka tahowa.

Ko tafiya nake ta yi waige ya yi min yawa 
Waige ne na tsarguwa ya hana minni nutsuwa 
Dukannin majalisa na wuce zan yi tsarguwa 
Zunɗe na kawai suke sunai minni daƙuwa. 

Bayan shekara takwas sauka ta da mulkawa 
Ba sauran abokanan gaba sai a 'yan uwa 
'Ya'yana da masu aurena na ta zaƙuwa 
Kullum bani lafiya gara a kai ni kushewa. 

Cuta ta kala uku ba waraka ba mutuwa 
Ga cutar hawan jini ta saka sashi mutuwa 
Sannan ga diabetes ga tibi yana zuwa 
In na saida kaddara kan sati fa ba uwa. 

Ƙarshe dai in baku labari kun ji 'yan uwa 
An hana kai ni hospital an girke ni ƙoƙuwa 
Kullum magani na Hausawa an ka jiƙawa 
Na alkinta kaddara kar na mace su yi kuwwa. 

Wannan shi yasa na ɗau waraƙa ta nake yi wa 
Dangi 'yan uwa nasiha kan wagga rayuwa 
Saƙon nan a kai wa Alan Waƙa na Kanawa 
Ga saƙo ya isuwa ga masoya da 'yan uwa. 

Me aure da duniya kai aniyar shirin hawa 
Hawa goɗiya da sirdi fili na sukuwa 
Ba ta gwani a sukuwa ko kai ne gwanin hawa 
Ran da ta tashi yarda da kai sai ta kai ka ƙoluwa. 



Post a Comment (0)