Sahabban Annabi (ﷺ) Sun Tsira Daga Shiga Wuta



Ramadaniyyat 1442H [29]

Dr. Muhd Sani Umar (Hafizahullah)

Sahabban Annabi (ﷺ) Sun Tsira Daga Shiga Wuta

1. Allah (SWT) yana cewa: (Kuma ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku yayin da kuka zamo abokan gaban juna sai Ya hada tsakanin zukatanku, sai kuka zamo 'yan’uwan juna a sakamakon ni'imarsa, a da kuma kun kasance a kan gabar ramin wuta sai Ya tserar da ku daga gare ta.) 
2. Wannan ayar tana nuna halin da sahabbai suke ciki a da kafin zuwan Musulunci, sannan tana bayanin ni’imar da Allah ya yi musu bayan Musulunci, ya tserar da su daga hallaka.
3. Saboda haka sahabbai wata al’umma ce da Allah ya yi wa ni’ima, suka zama ‘yan’uwan juna, ya kuma hada zukatansu, kuma ya tserar da su daga shiga wuta. Don haka idan wani ya zo ya ce sun yi ridda za su tafi wuta, to ya karyata fadar Allah ne da ya ce “kuma ya tseratar daku daga fada wa cikinta (wuta)”. Idan Allah ya ce tserar da su daga wuta, to yaya kuma wani zai zo ya ce za su shiga wuta, ko sun yi aikin 'yan wuta? Babu shakka wannan karyata Alkur’ani ne a fili.
4. Sannan wannan ni’ima da Allah ya fada cewa ya yi musu, ni’ima ce da suka gan ta a fili, saboda a kansu ta faru. Don haka duk al’ummar da za ta zo daga baya, idan tana so ta samu wannan ni’imar sai dole ta bi hanyar da suka bi suka samu, watau shi ne yin imani.
5. Hakanan wannan ni’imar ba ta rabu da su ba, har Annabi (ﷺ) ya yi wafati ya koma ga Allah, ni’imar nan na tare da su, kamar yadda Allah ya ce: (A yau Na cika muku addininku, kuma Na cika muku ni’imata, kuma Na yardar muku Musulunci ya zamo shi ne addininku.) [Ma’ida: 3] 
6. To wannan ita ce ni’imar da Allah ya cika musu, watau ya mayar da su suka zama al’umma daya, al’umma da kowa ya san da zamanta a duniya a halin yanzu, wanda a da can babu wanda ya san da zamansu, idan ma an tuna su, to ana tuno wata al’umma ce kaskantacciya da ba ta da wani abu na cigaba da za ta iya kawo wa a cikin rayuwar dan’adam, to sai ga shi kuma sun dawo wata al’umma wadda kowa ke shayinta a fadin duniya.
7. Saboda haka wannan ni’ima Ubangiji ya cika musu ita, ya kuma tserar da su daga wuta, don haka sun samu wannan shaidar cewa, su dai Allah ya tserar da su daga wuta, ya kuma cika musu wannan ni’ima. Yayin da wani zai zo ya bata martabar sahabban Annabi (ﷺ) kamar yana karyata wannan ni’ima ce da Allah ya ce ya yi musu, da kuma cewa bai cika musu ita ba, bai kuma tserar da su daga wuta ba, to ka ga babu shakka duk wani mai hankali ba zai yarda da shi ba. Saboda wannan magana ta shi ba a Alkur’ani ya ciro ta ba, daga ba ya ya samo wannan magana ta bata sahabban Annabi (ﷺ).

https://t.me/miftahul_ilmi
Post a Comment (0)