SAKO ZUWA GA MASU MATA DAYA...

SAKO ZUWA GA MASU MATA DAYA...
-----------------------------------------




*IBN SINA* yana cewa:
Idan mutum ya zama yana da mata daya zai ga jarraba a gaggar jikin sa da rayuwar sa.

zaka ga tsufa ya riske shi da kuruciyar sa,
Zai dinga yin ciwon kashin bayan sa da kashin wuyan sa da Kuma ciwon gabobin sa.

Zai dinga yawan debe kauna!
Zai zama Mara dabara!
Fara'ar sa zata tafi,
Zai zama mai yawan bacin-rai da koke-koke.

*ALQADI ABI MAS'UD* yana cewa:
Wanda duk ya kasance yana da mata daya bai dace yayi alqalanci ba, bai dace Kuma yayi sulhu tsakanin mutane ba.

*IBNU HAYYAN ATTAUHIDY* yana cewa:
Na ga mutanen da basa zama da duk Wanda yake da mata daya domin suna daukar sa yana cikin kananan mutane.

*IBNU KHALDUN* yana cewa:
Na lura da wata al'umma halakakkiya sai na gano al'adar su itace ka kasance da mace daya.

*AL'ABID IBNU MAISAR* yana cewa:
Ibadar mutum bata daidaituwa matukar dai mata daya ce da shi.

Aka ce da *MA'AMUN BIN HARUNA RASHID*
lalle a garin basara akwai wasu mutane mutum mai mutumci a cikin su shine mai mata daya!
Sai yace:
Wadannan ba mutane bane domin sun sabawa tunani mai kyau sannan sun sabawa sunnah ai mutum mai mutumci shine mai mata da yawa.

Akace da *IBNU YUNUS AL'MUZNY*
Me yasa yahudawa basa auren mata da yawa?
Sai yace:
Su wadannan mutane ne da Allah ya tabbatar musu da kaskanci da bada haraji kuma suka dawo da fishin Allah.

Akace da *ABU MA'ARUF AL'KURKHY*
Meye hukuncin mutane da basa aura sai mace daya! Suna ganin hakan gudun duniya ne?
Sai yace:
Babu komai ga irin wadannan mutane su din mahaukata ne domin duk yadda suka kai wajen gudun duniya basu kai rabi-rabin Sayyadina Abubakar da Umar da Usman da Aliyu wajen gudun duniya ba.

An tambayi *IBNU FAYYADH*
Kan mazajen da suke da mata daya!
Sai yace:
Wadannan matattu ne da suke ci suke sha suke numfashi.

Yayin da aka shugabantar da *IBNU ISHAQ AL' NAISABURY*
Sai ya dinga hana kyauta ga mai mata daya!
Sai aka ce da shi:
Me yasa Ka aikata haka?
Sai yace:
Wannan dukiya ce ta Allah bazan bayar da ita ga wawaye ba.

*IBNU ADA'ULLAHI* yana cewa:
Mutanen da suke da mata daya basa tafiya akan sunnar manya (yana nufin sunnar Annabi SAW da Sahabban sa) Kuma muna lissafa su cikin kananan mutane.

Yayin da *TAQIYYUDDINI AL'MUZNY*
Yaje garin sarmaqanda a matsayin malami Sai mutanen garin suka ce da shi:
Akwai wadansu mutane kowane mutum a cikin su matar sa daya!
Sai yace:
Anya kuwa wadannan musulmai ne?
Sai yayi musu wa'azi ya shiryar da su, ba'a fice wata daya ba Sai da aka daura auren mutane dubu uku acikin su!
Har Sai da ya zamana babu wata budurwa ko bazawara a garin sai da tayi aure.

*IMAMUL HUSRY* 
Yana cewa:
Yayin da Allah a cikin qur'ani ya ambaci aure sai ya fara da ambaton mace biyu sannan uku sannan hudu, sannan ya ambaci mace daya a karshe saboda tawayace ga cikar kamalar namiji.

MADALLAH GA MAI YAWAITA MATAN AURE
Post a Comment (0)