SHA'AWA SHA'AWA SHA'AWA!!
******************************
Da yawa daga cikin mutane suna dora laifin karkacewar dabi'unsu akan "Sha'awa". Suna cewa wai ita ce ta rudesu.
To ita dai sha'awa wata siffah ce ta kamalah (wato alamar cikar Mutuntaka) wacce Allah ya halicci 'Dan Adam da ita.
Idan 'Dan Adam ya zamanto babu ita ajikinsa, to lallai ya samu naqasu kenan. Domin ba zai iya cika wasu ayyukan da sauran 'Yan Adam (har Annabawa) suke yi ba. Wato shine aure da kuma haihuwa.
Ita sha'awa azuciya take amma tana da babbar alaqah tsakaninta da sauran gabobin jiki. Musamman idanuwa da hanci da hannaye.
Wato takan motsa ma mutum aduk lokacin da idanuwansa suka kalli irin abinda zuciyar take son gani. Ko kuma duk lokacin da hancinsa ya shaki wani irin Qamshin da zuciyarsa ke son ji, ko kuma yayin da hannuwansa suka ta'ba wani abu wanda zuciyar ke son ta'bawa.
Wannan yasa Allah gwani mai hikima ya umurci Muminai Maza da Muminai Mata cewa su runtse idanuwansu, wato ya haramta musu kallon duk abinda bai halatta garesu ba.
Sannan Annabi (saww) ya tsoratar da Muminai daga ta'bawa ko shafar duk wani jikin da bai halatta garesu ba.
Kuma Annabi (saww) ya haramta kebancewa atsakanin duk mutanen da ba Miji da Mata ko kuma Muharraman juna ba.
To amma matasan zamani duk sai sukayi burus da wadannan umurnin wai saboda wayewa. Sun saki linzamin idanuwansu, suna kallon tsaraicin Mata, suma Matan suna kallon tsaraicin Maza ko dai afili ta hanyar Qura ido, ko kuma a internet, ko kuma acikin wayoyin salula.
Sannan chudanya tsakanin Maza da Mata ba'a dauketa amatsayin wani babban abu ba. Ko a ina ma yi ake. A Motocin haya, gidajen biki, Makarantu, Ofisoshi, da sauransu.
Duk wanda ya saki linzamin idanunsa kuwa, lallai dole zuciyarsa ta rinjayeshi zuwa ga aikata sa'bo, ko kuma tunanin yin hakan.
Ya kamata lallai Matasa muji tsoron Allah Mahaliccinmu wanda yayi mana ni'imar gani da ji da fahimtar harshe. Domin hakika Ubangiji yana tare damu ko yaushe ako ina. Kuma akwai ranar da zai tashemu domin tambayarmu akan kowacce ni'imar da muka mora daga gareshi.
Ka sani cewa wannan idon naka da kake kallon fina-finan batsa dashi, Watarana shi zai yi magana agaban Zatin Ubangijinka, kuma zai fadi dukkan abubuwan da ka kalla dashi.
Haka ma hannayenka da Qafafunka duk zasuyi bayanin irin ayyukan da ka gudanar dasu.
Al'aurarka ma ba za'a barta abaya ba.. Zatayi magana awannan ranar, zata bada shaida akanka.
Ya Allah ka shiryemu ka Qara mana tsoronka, ka kiyayemu daga sa'ba maka. Ameeen.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP 16-11-2016 (16-02-1438).