🌹SHAWARATA GARE KI 'YAR UWATA.
Ki yi hattara da likitocin yanar gizo, domin tabbas za su kai ki su baro.
Lafiya uwar jiki ce, kina buqatar lafiya don bauta wa Mahaliccinki, gudanar da al'amuran rayuwa tare da 'kara kima a idon Mai gidanki.
Mace tana da rauni, halitta ce da ko yaushe jikinta yake buqatar gyara da kulawa. Da wannan ne ake amfani wajen cutar da su ta hanyar magunguna.
Za ka samu mutum ba shi da wani ilimin da yā shafi harkar lafiya, amma ya buďe group wai shi yā zama mai bayar da magani da shawarwari a kan kula da lafiya (health therapist), kuma majority na clients da customers nashi matane, saboda su suka fi raina kan su?
Akwai wata mace mai ciki da ta amshi maganin ciwon māra wajen wani mai group ďin bayar da magani, 'karshe dai da ta sha maganin jini ya 6arke mata, hakan ya yi sanadiyar zubewar cikin. Garin nemo 'kiba an nemo rāma! 😔
'Yar uwa, abin da ya fi shi ne idan ba ki da lafiya ki je asibiti likita ya duba ki. Amma wani likita ne zai kasance kusan koda yaushe online a yanar gizo? 🤔
Bā ina kushe dukkan masu magani bane da suke sayarwa a yanar gizo, amma wajibine a yi taka tsan-tsan wajen sanin wanda ya dace a siya magani a wajensa.
Magani zai iya amfani a jikin wata, ke kuma idan kin sha ya cutar da ke. Akwai _Drug allergy,_ wanda ke faruwa sakamakon shan maganin da be dace da _immune system_ na jiki ba, yana haifar da ciwo mai tsanani har ya yi barazana ga rai, a duk shekara a Najeriya ana samun irin wannan cases fiye da miliyan ďaya da dubu ďari biyar (1.5million). Kafin ki shā magani ki duba ingredients da aka haďa maganin da shi ki ga sun dace da jikinki, wannan ya sa ganin likita yake da amfani.
Sannan akwai kalolin medications da bā a yin amfani da su a lokaci ďaya domin za su iya zama masu cutarwa ga jiki duk da kasancewar su magani, shiyasa kafin likita ya rubuta maki magani zai tambaye ki shin kina amfani da wani maganin ne? Kin ga zai yi wuya masu bayar da magani a yanar gizo su tsaya binciken wannan.
Don haka lallai ya dace a kula, kada kawai daga kin ga an yi post cewa a haďa abu kaza da kaza yana maganin ciwo kaza, kawai sai ki je ki yi ba tare da neman shawarar masana lafiya ba, yin hakan bā dai-dai bane.
A kula da lafiya yar uwa!
Allah Ya ba mu lafiya mai amfani. 👏🏾
.
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*08166650256.*
*📚Irshadul Ummah WhatsApp.*