SHIN WAI AKWAI WADANDA SU BASU DA SA'AR RAYUWA NE?



SHIN WAI AKWAI WADANDA SU BASU DA SA'AR RAYUWA NE?

https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV

*TAMBAYA*❓

Assalama alaikum Allah ya karawa mlm lpy mlm dan Allah akwai mutanen da su a rayuwar su komai zasu samu indai mai mahimmanci ne sai sunsha wahala susai??


*AMSA*👇

Wa alaikumus salamu wa rahmatullahi wa barakatuh. Alhamdu lillahi rabbil alamin wassalatu wassalamu ala rasulillahi wa ala alihi wa sahbihi ajma'in. 

Da farko dai mu sani cewa samu da rashi na alkhairi ko na sharri, kaddara ce ta Allah da ya rubuta ma bawa shekaru dubu hamsin kafin a halicci duniya.

عَنْ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ عَمْرِو بْنِ الْعَاصِ قَالَ: سَمِعْتُ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَقُولُ: ((كَتَبَ اللَّهُ مَقَادِيرَ الْخَلاَئِقِ قَبْلَ أَنْ يَخْلُقَ السَّمَوَاتِ وَالأَرْضَ بِخَمْسِينَ أَلْفَ سَنَةٍ- قَالَ- وَعَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ)). 

Bayan haka ya rubuta ma bawa iyakar arzikin sa tun yana mahaifa kafin a busa masa rai. Duba da wannan, babu yadda bawa zai kubuta daga abinda yake mukaddari. 

2018 - 890 - «إن أول ما خلق الله القلم فقال له: اكتب قال: يا رب وما أكتب؟ قال: اكتب مقادير كل شيء حتى تقوم الساعة من مات على غير هذا فليس مني» .
(صحيح) ... [د] عن عبادة بن الصامت. شرح الطحاوية 271.

Arzikin kowane bawa na hannun Allah 

(۞ وَمَا مِن دَاۤبَّةࣲ فِی ٱلۡأَرۡضِ إِلَّا عَلَى ٱللَّهِ رِزۡقُهَا وَیَعۡلَمُ مُسۡتَقَرَّهَا وَمُسۡتَوۡدَعَهَاۚ كُلࣱّ فِی كِتَـٰبࣲ مُّبِینࣲ)
[Surah Hud 6]

Bayan haka Allah ke raba arzikin ga bayi, amma ta hanyar da ya ga dama

(أَهُمۡ یَقۡسِمُونَ رَحۡمَتَ رَبِّكَۚ نَحۡنُ قَسَمۡنَا بَیۡنَهُم مَّعِیشَتَهُمۡ فِی ٱلۡحَیَوٰةِ ٱلدُّنۡیَاۚ وَرَفَعۡنَا بَعۡضَهُمۡ فَوۡقَ بَعۡضࣲ دَرَجَـٰتࣲ لِّیَتَّخِذَ بَعۡضُهُم بَعۡضࣰا سُخۡرِیࣰّاۗ وَرَحۡمَتُ رَبِّكَ خَیۡرࣱ مِّمَّا یَجۡمَعُونَ)
[Surah Az-Zukhruf 32]

Wani ya same shi ta hanya mai sauki, misali kamar wanda za'a mutu a bar masa gadon milyoyin kudi, wani lokaci, tun yana yaro. Wani kuma ya rayu yana wahalar nema kuma ya samu arziki dan kadan. Haka al'amarin yake, ko a cikin dabbobi, kwari, tsuntsaye da sauran halittun Allah, wasu ya kaddara masu saukin samu wasu kuma akasin hakan.

Saboda haka kar ya samu damuwa don wasu suna samun irin abinda yake samu cikin wahala, cikin sauki. Wannan wahala da yake wajen neman abin alkhairi ta hanyar halal, yana da lada. Sannan ko sata a wasu lokutta barayi suna shan wahala, wani lokaci kuma tayi masu sauki. Don haka wannan ba ma'auni bane na hukunta rashin sa'a ko da'a ga Allah da za'a yiwa wani mutum.

Daga karshe dai wannan na tattare da mashi'ar Allah wacce ba wanda ya isa ya tambaye Shi, yaya haka? Allah ya saukaka mana al'amuran mu na duniya da lahira. 

Wallahu ta'ala a'lam

 *_Amsawa_* :

 *Malam Aliyu Abubakar Masanawa*

‎Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
 *_Group Admin: ▽_*
 *MAL. HAMISU IBN YUSUF*
Post a Comment (0)