TANBIHI AKAN HANYOYIN GAMSAR DA JUNA A TSAKANIN MA'AURATA



*SIRRIN MALLAKAN MIJINKI*


Tanbihi Akan Hanyoyin Gamsar Da Juna Tsakanin Ma'aurata

A matsayinki na uwar gida abin da zaki fara yi wajen gamsar da mijinki shi ne nuna masa shauki da zumudin son yin jima’i, kada ki nuna jin kunya domin nuna masa zumudi wajen saduwa zai ba shi damar shirya kansa da kuma yin zumudi shi ma, wanda idan haka ta faru kin taka wani mataki na gamsar da shi domin kin motsa masa sha’awarsa.

Yayin jan hankalinsa ki yi kwalliya da ado, ki fesa turare mai sanya shauki, sannan ki rika yauki da shagwaba da kuma kisisina.

Hanyar jan hankalin miji ta hada da rausayar da canza murya, sanya tufafin da za su fitar da sura don hakan ya kara janyo hankalin miji.

Murmushi, yin kalamai cikin tausasa murya, wani lokaci mai cike da sigar rada tana haifar da motsuwar sha’awar mazaje. Yin kalaman barkwanci, yin wasa ga miji da sauransu.

Wabillahi Taufiq.

Rubutawa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

Gabatarwa: *Abu Imam (Auwal Abdullahi)*

*- Zauren Macen Kwarai-*

*. Ga masu buqatar shiga Zauren Macen Kwarai sai su tura da cikeken sunansu tare daga in da take, ta wa'innan numba;* 👇 👇 👇

08162268959,08038902454
Post a Comment (0)