SHIN YA HALATTA MUTUM YA SHA MAGANIN ƘARIN ƘIBA?



Tambaya
:
Shin ko ya halatta mutum ya sha maganin ƙara ƙiba idan ya kasance ramamme ne shi?
:
Amsa
:
Dangane da hukuncin shan magani domin neman ƙara ƙiba a jiki ko kuma dan saboda wani sashe na jikin mutum ya ƙara girma kamar misali mace ta sha magani da nufin nonuwanta ko kuma ɗuwawunta su ƙara girma. Bayanin da Malamai sukayi akan haka shi ne, akwai wanda ya halatta a gareshi ya sha maganin ƙara ƙiba, akwai kuma wanda haramun ne a gareshi ya sha wannan magani, wato ya danganta ne da niyya ko sababin da yasa za a yi amfani da wannan magani.
:
Idan ya kasance mutum yana da wani aibu ko naƙasa a jikinsa wanda ya wuce irin wanda aka saba ganin mutane da shi a bisa al'ada, kamar misalin mutumin da yayi accident wani sashe na jikinsa ya lalace ko wanda haƙoransa suka fito waje da yawa zaƙo-zaƙo, ko ya kasance mutum a rame yake sosai irin ramewar da ta wuce wadda aka saba gani a al'ada, kuma ko da yana cin abinci mai gina jiki haka yake ba ya ƙaruwa, to a yanayi irin wannan Malamai sukace idan masana kiwon lafiya (Likitoci) suka bashi shawarar cewa ya sha maganin ƙara ƙiba to ya halatta ya sha, ko kuma ayiwa Mutum aiki dan a kawar da wannan aibu ko naƙasar da ke tare dashi, domin an yi masa haka ne da nufin a kawar da wannan naƙasa da ke tare da shi ne kawai dan haka babu laifi.
:
Amma idan ya kasance babu wata naƙasa a jikin mutum irin naƙasar da ta wuce wadda aka saba gani a bisa al'ada, sai dai kawai mutum zai sha maganin ƙara ƙiba ne da nufin ya ƙara masa kyau, ko kuma mace ta sha magani da nufin ɗuwawunta su ƙara girma ko da nufin nonuwanta su ƙara girma idan ya kasance ƙanana ne, ko kuma a rage musu girma idan sun kasance nonuwanta manya ne sosai domin kawai ta ƙara kyau dan tariƙa burge mutane: ko kuma saboda kasancewar mutum ba shi da jiki sosai a cikin abokansa sai ya ke so ya sha magani da nufin jikinsa ya koma irin na su, da dukkan wani wanda zeyi amfani da wani magani da nufin ya ƙara kyau bawai wata larura bace mai tsanani tasa ya buƙatu da dole sai yayi hakan ba, to dukkan waɗannan abubuwa da makamantansu haramun ne aikatasu. domin ya shiga ƙarƙashin hukuncin masu jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ) domin dama shaiɗan ya faɗa cewa sai ya umarci mutane suna jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ) kamar yadda Aʟʟαн(ﷻ) Ya faɗa a cikin wannan aya:
:
"ولآمرنهم فليغيرن خلق الله"
Sai na umarcesu da su riƙa jirkita halittar Aʟʟαн(ﷻ)
:
Dan haka abu ne mai matuƙar haɗari haka kawai mutum yace zai sha maganin ƙara ƙiba da nufin ya ƙara kyau, ya kamata a sani cewa, duk fa yadda mutum ya kai ga rena kansa to a hakan shi abin sha'awa ne a wajen wasu mutanen, haka nan kuma duk yadda mutum ya kai ga jirkita halittarsa da nufin ya ƙara kyau, to ko rabin-rabin kyawun wani ba zai taɓa kaiwa ba. Dan haka garama mutum ya haƙura da yadda mahaliccinsa ya halicceshi sai ya zauna lafi lafiya.
:
​​※(шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ)※​​
:​​▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂​​
              ​Daga Zaυren​
             ​Fιƙ-нυl-Iвadaт​
​​▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂​​
           ​Mυѕтαρнα Uѕмαn
              ​08032531505​
​​▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂▂​​
​​Doмιɴ ѕнιɢα ѕнαғιɴмυ dαкє ғαcєвooк ѕαι αѕнιɢα wαɴɴαɴ lιɴк кαwαι αyι ""lιкє""👇🏾​​
:
https://m.facebook.com/fiqhul.ibadat
Post a Comment (0)