TUMBIƊO


TUMBIƊO

Alamu dai na nuna cewa tumbiɗo mai tumbuɗin matsabbai a tuƙullumar taliƙe lalitar masu ba wa idanu abinci ya kusa gama tumbuɗe iya madarar da ya hambaɗa. Wannan batu kuwa ya biyo bayan sahihan batutuwa ne da suka nuna irin rikita-rikitar da aka yi wajen ƙarawa kafcensa mai suna Rarumar Maƙiya da ya fita a kwanakin baya yawan alƙaluman damin hauron da ya tattara. In ba ku manta ba dai a 'yan shekarun nan da suka arce, takwarorinsa wato shamharu da Amiru sun fuskanci komai ba ya wajen samun kasuwancin aiyukansu, in da hakan ya sa mabiyan salmanu samɓalin saɓalula kuma tumbiɗon tuƙullumar tara damin hauro suke ganin cewa gwanin na su fa ya fara kerewa sa'a. Kwatsam ana cikin haka kuma sai ga shi wannan badaƙalar ta kunno kai. Shin ko shima ya kusa gama na shi tumbuɗin ne? Masu iya zance dai na cewa: "kaza bar ganin ana jan hanjin 'yar uwarki kina dariya, watarana naki za a ja". Kuma mallam Bahaushe na cewa; "shure-shure ba ya hana mutuwa". In da sauran suka je, shima in ƙaddararsa kenan sai ya je. Amma ba a bakina kuka ji ba. Ehe!

Na arce.

©️✍🏻
 Jamilu Abdulrahaman
   (Mr. Writer) 
  Haiman Raees 
Haimanraees@gmail.com
Post a Comment (0)