༺ SALLAN DARE (Qiyamul-laili) ༺
πSallan dare tana sanya ka daga cikin bayi na gari.
πAkwai lada 'boyayya ga wanda yake tsayuwar dare.
πSallan dare tana d'aga ka zuwa matsayin masu gode Allah.
πSallan dare tana tseratar da kai daga wuta
πSallan dare tana d'aga ka izuwa wadanda suke masu biyayya ga Allah
πSallan dare tana sanya ka kusa da Ubangijin halittu
πSallan dare lokaci ne na amsa Addu'a
πIta Sallan dare Sababi ne daga cikin sabubban shiga Aljannah
πSallan dare tana sanya ka daga cikin wadanda Allah yake son su
πWanda ya yi tsayuwar dare shida matarsa Addu'ar Annabi s.a.w zata same sa
πSallan dare tana sanya ka acan saman Aljannah (ka samu gida a saman Aljannah)
πDaukaka/darajan ta mumini shine Sallan dare
πYana burge Allah ga wani zai yi tsayuwar dare, kuma Allah yana dariya agare shi (dariyan jin dad'i).
πMe tsayuwar dare kusa yake da Allah Ta'ala
πSallan dare tana warware kullukan shaid'an
πSallan dare tana sanya ka shiga Aljannah ba tare da zafin wuta ya same ka na.
πYin na rige wajen Sallan dare.
Duba littafin (Dariqus-salihin) malam Waheed Abdus-Salam Baliy
Allah Ta'ala ka sanya mu cikin bayi masu wannan ibada mai tsada tare da kyakkyawan niya (Amin)
# Zaurenfisabilillah
Telegram: https://t.me/Fisabilillaaah
Facebook:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/