WA NENE MAI AZUMI NA GASKIYA?

WA NENE MAI AZUMI NA GASKIYA?


Ibnul Qayyim RA yace: 

"Mai azumi shine wanda gabbansa suke azumi daga ayyukan sa6o, harshensa yake azumi daga karya da alfasha da maganar zur, cikinsa yake azumi daga abinci da abin sha, farjinsa yake azumi daga jima'i.

Idan zai yi magana ba zai  fad'i abin da zai raunata azuminsa ba, haka ma in yayi aiki ba zai aikata abin da zai bata azuminsa ba, sai maganganunsa duka suke fitowa masu amfani kuma nagari, haka ayyukansa suna a matsayin qamshi da yake shafar wanda ya zauna da mai dauke da Almisk, haka wanda ya zauna da mai azumi yake amfana da zama dashi, kuma ya amintu daga maganar zur, karya da zalumci.

Wannan shine azumin da a ka shar'anta mana ba kawai kamewa daga cin abinci da abin sha ba.

Azumi shine azumin gabbai daga laifuka/zunubai, da azumin ciki daga cin abinci da abin sha, kamar yanda abinci da abin sha  ke yankeshi da bata shi(azumin), to haka zunubai suke yanke ladanshi suke lalata amfaninsa, su maidashi kamar wanda bai yi azumi ba!.

[الوابل الصيب 32/31]

#Zaurandalibanilimi

Telegram:
https://t.me/Zaurandalibanilimi

Instagram: https://www.instagram.com/p/B_NuiocDqSw/?igshid=3hzyza1v460v
Post a Comment (0)