Wannan rayuwar tana ba ni tsoro...
Idan ina cin karo da yadda tarbiyya take ci gaba da lalacewa a wannan zamani, tabbas abin yana ba ni tsoro, kuma yana jefa ni cikin damuwa.
Yadda *Zina* da sauran dangoginta suke yaɗuwa cikin al'ummarmu Wallahi abin firgici ne!
Yanzu ba ka da damar ka buďe baki zā ka yi shaidar wata, sai ka ji an ce ai ga abin da take aikatawa 😢
A da an fi zargin 'yan talla da zubar da budurci a titi kafin aure, amma yanzu ba matan colleges da universities kaďai ba, har 'yan Islamiyya suna afka wa cikin wannan mummunan ďabi'a.
Yarinya 'karama 'yar secondary school ta san ta yi zina, yarinya yar Islamiyya wacce da ka gan ta ka ga wacce ta fito daga gidan mutunci, amma shaiďan ya rinjaye ta zuwa wannan masifa.
Yanzu in dai ka tashi yin aure ka shiga fargaba kenan, kada ka ďauko karuwar layi ka ajiye wa yaranka a matsayin uwa. 😔
Mazan ma da yawansu sun yi nisa da shiriyar Musulunci, bā su yin soyayya da yarinya a gama ba tare da sun yi 'kokarin lalata rayuwarta ba.
Iyaye sun fi mayar da hankali wajen tarbiyyar yara mata, bayan kuma mazan ke sabbaba annobar.
Zina ta zama ruwan dare, ni da kai mun san hakan. Amma a haka muke tunanin Aʟʟαн(ﷻ) ba Zai jarabce mu ba, a haka muke tunanin fitintinu da masifofi ba za su afko mana ba?
Yā Allah na ji labarin irin azabar da ka tanadar wa mazinata. Yā Allah! Ka ji tausayinmu, Ka nisanta mu daga zina da dukkan dangoginta. Yā Allah! Kada ka cuďanya zuriyarmu da mazinata, yā Allah Ka ba mu māta salihai.👏🏾
.
*✍🏽Ayyub Musa Jebi.*
*2348166650256.*