SHAFA FUSKA A BAYAN ADDU'A

*SHAFA FUSKA A BAYAN ADDU'A*



Assalamu alaikum ga tambayata kamar haka. Mene ne hokuncin shafa fiska idan an idar da adduah?

*Amsa*

SHAFA FUSKA A BAYAN ADDU'A.

As-salamu alaikum.

1) Daga hannuwa a wasu lokutan addu'a Sunna ce a wajen da shi Annabi ya daga su. Banda tofawa da shafar fuska ko kirji a karshe. [SAHI'HU ABI DAWUD; 1/278, MAJMU'U FATA'WA; 22/519].

2) Akwai hadisai na shafan fuska a bayan gama addu'a daga Sayyiduna Umar cewa Annabi ya na yin hakan, haka ma daga Abdullahi Ibnu Abbas cewa Annabi ya yi umurni a aikata, amma duk masana hadisi sun tabbatar ba su inganta ba. [DHA-I'FU ABI DAWUD; 1485, DHA-I'FUT TIRMIZY; 3386, DHA-I'FU IBNI MA'JAH; 778, DHA-I'FUL JA'MI-I; 492, 3274, 4412, 6226, IRWA'UL GALIL; 2/180, 433]

3) Malamai masu yawa sun ki shafawar, daga cikinsu akwai Al-Imam Malik da Al-Imam Ahmad bin Hambal, ibnu Taimiyya, Ibnul Qayyim, AbdulAziz Bin Baz, akwai ma Izzud-Din bin Abdis-Salam mai ganin cewa bidi'a ce. [MAJMU'U FATA'WA; 22/519, BADA'I-UL FAWA'ID; 5/214, FATA'WAL LAJNA; 24/215, FATA'WA IBNI BAZ; 26/138]

4) Wasu manyan masana hadisi kuma sun ce babu laifi don yawan hadisan shafawar kamar An-Nawawi, Ibnu Hajar, As-San-a'ni, Ash-Shawka'ni, Al-Mina'wi, akwai ma labarin cewa wasu sahabbai sun yi kamar; Ibnu Umar da Ibnuz Zubairi, [AL-ADABUL MUFRAD; 906, AL-MAJMU'U; 4/487, KASHSHA'FUL QINA; 1/420, SUBULUS SALAM; 4/709, FAYDHUL QADIR; 5/176].

5) Mafi 'karfin hujja shi ne cewa shafa fuska bai inganta ba, kuma bari ne ya fi, amma kada a kushe ma wanda ya aikata, don ya na da magabata. [FATA'WA IBNI UTHAYMIN; 14/162]

_*Amsawa Sheihk Abdurrazak Yahaya haifan*_

8/11/1442 19/6/2021.
.
.
https://t.me/irshadulummah1
Post a Comment (0)