*Ramadaniyyat 1442H [6]*
Alakar Sahabbai Da Annabi (ﷺ): Jigon Nasara Da Tubalin Gina Zukata
*1.* _Sahabban Annabi (ﷺ) ba su ci nasara a kan Farisawa da Rumawa ba saboda yawan da suke da shi, don ba za a hada yawan sahabbai da suke da runduna mai mayaka dubu talatin (30,000) ba, da wadanda suke da runduna mai mayaka dubu dari da hamsin (150,000). Sahabbai wadanda suka fito daga sahara a kan dawakai, sun fito sun ja daga da fito-na-fito da wannan runduna mai dauke da manyan makamai da mayakan da suka dade a harkar yaki, wadanda kuma suka samu ingantaccen horo mahaya giwaye. Amma duk da haka sahabban nan suka ci nasara a kan wannan babbar runduna mai tarin yawa._
*2.* _Saboda haka ba su sami wannan nasara ba saboda yawansu ko yawan kayan yakinsu ba, a’a sun ci nasara ne saboda karfin imanin da suke da shi da ruhin da ya gina musu zuciya da kuma tarbiya da jajircewa da suka samu daga Annabi (ﷺ)._
*3.* _Hakanan suka ci gagarumar nasara wajen tafiyar da jagorancin dukkan wata al’umma da suka yaka suka kuma ci nasara a kansu. Suka yi musu mulki mai cike da adalci._
*4.* _Wannan ta sa zukatan da suke cike da qin su suka dawo suna son su, mutane suka rika shiga addinin Musulunci dodo-dodo, kungiya-kungiya a dalilin abin da suka gani na kyawawan dabi’unsu, da abin da suka gani na adalci da mutuntaka, wanda ba su taba ga irinsa ba a baya, tare da cewa a da ‘yan’uwansu ne suke mulkar su ko wata daula kafaffiya._
*5.* _Shi ya sa a kundin tarihi duka, idan aka cire annabawan Allah, to babu wata al’umma da aka tava yi kamar sahabban Annabi (ﷺ)._
*6.* _Rayuwar waxannan sahabbai ta ta’allaka ne da Ma’aiki (ﷺ) gaba dayanta, kullum suna tare da shi; suna tare da shi a masallaci, suna kuma tare da shi a tafiye-tafiyensa da yake-yakensa da dukkan wani yanayi da suke ciki. Idanunsu na kansa a dukkan wani motsinsa; sun sa masa ido, sun kiyaye duk wani lamarinsa karami da babba, sun kiyaye yadda yake tafiya da yadda yake dariya ko murmushi, da yadda yake yin mu’amala da bako, da yadda yake mu’amala da matansa, kamar yadda suka kiyaye baccinsa da farkawarsa. Babu wani abu wanda ya shafi Annabi (ﷺ) da ba su kiyaye ba, ba don wani abu ba sai saboda yadda zukatansu suka ta’allaka da Ma’aiki (ﷺ)._
*7.* _Sun kasance suna bin sa har gida su yi masa tambaya, su hadu da shi a masallaci, su nemi sani daga wadanda suka san shi kari a kan abin da suka sani game da shi._
*8.* _Saboda haka rayuwarsu ta zama tare da wannan Annabi, domin su ne Allah (SWT) ya zaba don su dauko wannan sakon da wannan hasken da Annabi (ﷺ) ya zo da shi, zuwa ga al’ummun duniya da za su zo a bayansa._
*9.* _Wadannan suna daga cikin dalilan da za su sa duk wani mai hankali da tunani, ba zai yi tunanin cewa Allah (SWT) ya yi wa Ma’aikinsa zabin tumun dare ba._
_Rubutawa:- *Dr Muhd Sani Umar R/lemu*_
_Gabatarwa:- *Abu-Muhd*_
*_Darussunnah foundation_*
+2347030233318