DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 24



*_▪️📖♦️ DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 24 ♦️📖▪️_*

*_✍️ Yusuf Lawal Yusuf_*

*_بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ_*

إِذَا جَاءَ نَصْرُ اللَّهِ وَالْفَتْحُ ( ١) وَرَأَيْتَ النَّاسَ يَدْخُلُونَ فِي دِينِ اللَّهِ أَفْوَاجًا (٢) فَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ وَاسْتَغْفِرْهُ إِنَّهُ كَانَ تَوَّابًا (٣) النصر: (١-٣).

1. Idan nasarar Allah ta zo da kuma buɗe (Makka).
2. Ka kuma ga mutane suna shiga cikin addinin Allah ƙungiya-ƙungiya.
3. To ka yi tasbihi da yabon Ubangijinka, ka kuma nemi gafararsa. Lalle Shi Ya kasance Mai karɓar tuba ne. Suratun Nasri (1-3).

*_Tafsiri:_*
Allah (Subhanahu Wata'ala) ya buɗe Surar da yi wa Manzonsa (sallallahu alaihi wa sallama) albishir da samun gagarumar nasara da buɗe garin Makka, sannan zai ga mutane ƙungiya-ƙungiya suna ta shiga addinin Musulunci bayan a da suna gaba da shi.

An karɓo daga Abu Huraira (radiyallahu anhu) ya cw: Lokacin da wannan Surar ta sauja, sai Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama) ya ce: "Mutanen Yaman sun zo, masu sanyin hali. Imani Bayamane ne, fahimta ma Bayamaniya ce, hikima ma Bayamaniya ce." [Ahmad #7723].

Sai kuma Allah (Subhanahu Wata'ala) ya umarce shi da cewa, yayin da ya ga waɗannan abubuwa sun auku, to ya sani wannan alama ce mai nuna aikinsa na manzanci ya zo ƙarshe, sai ya duƙufa wajen yi wa Ubangijinsa tasbihi tare da gode masa bisa ga ni'imar nasara da cin garin Makka da yaƙi da ya ba shi, ya kuma nemi gafararsa, domin shi Allah mai yawan karɓar tuban bayinsa ne mai gafarta musu.

An karɓo daga A'isha (radiyallahu anha) ta ce: Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama) ya kasance yana yawan faɗar: Subhanallahi wa bi hamdihi wa astagfirullaha wa atubu ilaih, sai na ce: Ya Manzon Allah, na ga kana ta yawaita faɗar waɗannan kalmomi. Sai ya ce: "Ubangijina ne ya bayyana min cewa, zan ga wata alama a cikin al'ummata, idan na gan ta, to in yawaita faɗar waɗannan kalmomin, to haƙiƙa na gan ta ita ce (sai ya karanta wannan Surar, ya fassara 'buɗi' da buɗe Makka)." [Muslim 484].

An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (radiyallahu anhu) ya ce: Umar (radiyallahu anhu) ya tambayi sahabbai abin da suka fahimta daga wannan Surar sai suka ce, ana nufin buɗe garin Mada'in da cinye manyan fada-fada na Farisawa. Sai ya tambaye ni, ni kuma sai na ce: Misali ne aka ba Muhammad (sallallahu alaihi wa sallama), aka sanar da shi lokacin mutuwarsa ya yi." [Bukhari #4969].

*_Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:_*

1. Albishir ga Annabi (sallallahu alaihi wa sallama) da samun nasara a kan abokan gabarsa da buɗe garin Makka da shigar jama'a mai yawa cikin addinin Musulunci.
2. Nasara za ta ɗore ga Musulunci, kuma idan Musulmi sun ci gaba da riƙo da addininsu da gode wa Allah a kan ni'imominsa tare da yawan neman gafarar zunubansu, to nasara za ta yi ta ƙaruwa, Musulmi kuma suna ƙara samun izza, domin godiyar Allah sanadiyya ce ta ƙarin samun tagomashi daga gare shi.
3. Nuna wa Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama) kusantowar ajalinsa, domin rayuwarsa rayuwa ce mai daraja sosai, an kuma koyar da shi cewa, duk wani abu mai daraja da falala ana so a rufe shi da Istigfari kamar yadda aka yi umarni da yin Istigfari bayan gama salllolin farilla da bayan kammala tsayuwar Arfa, don haka shi ma Manzon Allah (sallallahu alaihi wa sallama) a nan sai aka umarce shi da yabo da godiya ga Allah da neman gafara, don a nuna masa ajalinsa ya zo ƙarshe, don haka ya shirya komawa ga mahaliccinsa Allah.

Tsakure Daga Cikin Littafin Fayyataccen Bayani Na Ma'anoni Da Shiriyar Alƙur'ani, Tafsirin Sheikh Dr. Muh'd Sani Umar Rijiyar Lemu.

*_Telegram:_* https://t.me/DDAMG

*_5th Rajab, 1442A.H (17/02/2021)._*
Post a Comment (0)