ALLAH YANA AMSA ADDU'AR DA KAYIWA MUTUM A BAYAN IDONSA
Manzon Allah ﷺ Ya Kwadaitar Da Mu Akan Yiwa Yan Uwan Mu Addu'a A Bayan
Idonsu,Kuma Yadda Allah Da Manzonsa Suka Umarcemu Mu Riqa Nemawa Yan Uwanmu Gafara,Manzon Allah ﷺ Ya Fadi Hakan A Hadisinsa.
¤manzon Allah ﷺ Yana Cewa: (Duk Wanda Yayiwa Dan Uwansa Addua A Bayan Idonsa,Sai Mala'ikan Da Yake Tare Da Shi Yace:Amin,Kaima Kana Da Kwatam Kwacin Abinda Ka Roka Masa)
@ﺭَﻭﺍﻩُ ﻣُــﺴْﻠِﻢ.
ﺍﻟـﻨـﻮﻭﻱ ﺭﺣﻤـﻪ ﺍﻟﻠﻪ ﺗـﻌﺎﻟﻰ :
Yana Cewa:
"Wannan Hadisin Yana Baiyana Mana Falala Da Matsayin Yiwa Dan Uwanka Addua Bayan Idonsa,Kuma Da Zakayi Adduar Ga Dukkan Musulmai Baki Daya Da Hakan Ya Sami Dukkansu Kuma Kaima Ka Sami Matsayi Da Falala Mai
Girma........".
Kuma Magabata Na Kwarai Sun Kasance, Idan Zasu Roki Allah Wani Abu,Sai Su Rokawa Yan Uwansu Irin Abinda Suke So Allah Ya Basu,Domin Wanda Yayiwa Dan Uwansa Addua A Bayan Idonsa,Allah Yana Amsa Wannan Adduar Kuma Shima Mai Adduar Allah Ya Abashi Irin Abinda Ya Rokawa Dan Uwansa".
@ﺷـﺮﺡ ﺻﺤـﻴﺢ ﻣـﺴﻠﻢ〙9/51 〙
ﺍﻟـﻌَﻠّﺎﻣَـﺔ ﺍﺑْـﻦُ ﻋُﺜَﻴْـﻤِﻴﻦ - ﺭَﺣِـﻤَﻪ ﺍﻟﻠﻪ:
Yana Cewa:
"Yiwa Yan Uwanka Addua A Bayan Idon Su,Alamace A Bayyane Daga Cikin Alamun Imanin Bawa,Saboda Manzon Allah ﷺ Yace: (Imanin Dayanku Baya Cika Har Sai Ya Sowa Dan Uwansa Irin Abinda Yake Soma Kansa)
Idan Kayiwa Dan Uwanka Addua A Bayan Idonsa,Ya Sani Ko Bai Sani Ba, To Wannan Alamace Ta Nuna Soyayya Da Fatan Alkhairi Agaresa.....".
@ﺷﺮﺡ ﺭﻳﺎﺽ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﻴﻦ〙 4 / 20 ، 21 〙
Allah Ne Mafi Sani
ALLAH INA ROKONKA DA SUNAYANKA KYAWAWA DA SIFFOFINKA MAFIYA KYAU, KUMA INA
TAWASSILI DA IMANIN DA NAYI DA KAI DA MANZONKA, YA ALLAH KA BIYAWA DUKKAN MUSULMAN DUNIYA BAKI DAYA BUQATUN SU NA ALKHAIRI, KUMA KA GAFARTA MASU DUKKAN ZUNUBANSU.
✍🏽Mustapha Musa Abu Aisha