HAQQOQI BAKWAI (7) NA ALQUR'ANI AKANMU
1● Yin tilawarshi haqiqanin tilawa.
2● Haddaceshi ko haddace abinda ya samu daga gareshi.
3● Mu san ma'anoninshi da tafsirinshi.
4● Yin tadabburinshi/lura da tunani cikin shi.
5● Mu ringa mudarasan shi tare da 'yan uwanmu.
6● Mu yi aiki dashi.
7● Mu koyar dashi.
شيخ محمد صالح المنجد/سلسلة نصف دقيقة بعنوان سبعة حقوق القرأن علينا.
☆★☆★☆
●Cikin haqqoqin Alqur'ani akanmu yin tilawarshi haqiqanin tilawa, karantashi kaman yanda aka saukar, sanin tajweedinsa, bama ko wane harafi haqqinshi, sanin mafitar kowane harafi, karantashi/rera shi da murya ko sauti mai dadi gwargwadon zaqin sautinka, karantashi anatse kuma cikin ladabi da lura da ma'anoninsa. kar mu qaurace mishi da sauransu.
●Lura/Tadabburin ma'anoninshi baya yiwuwa sai da sanin ma'anonin ayoyin wannan kuwa shine tafsiri.
●Sanin ma'anoninshi ko tafsirinsa da tadabburi shi ke taimakawa gurin mudarasarshi atsakanin juna. Manzon Allah SWA ya kasance suna yin mudarasar Alqur'ani shi da Jibrilu A.S.
MUDARASAR ALQUR'ANI
Wannan ya karanta wannan na saurare, sannan sai su yi musanyar abinda ke cikin wannan ayar na daga ilimi, ma'anoni, girmama Allah, abinda ya shafi wa'azi, tsoratarwa, kwadaitarwa, hukunce hukunce, qissoshi, fa'idoji, falalolin Allah ga bayinSa..........dss.
Shaykh Muh'd Saleh Almunajjid
Allah ya sanya mu cikin masu sauke wadannan haqqoqi na Alqur'ani.