BAMBANCI {19}



BAMBANCI {19}

Kafin mutum yafara magani dole ne sai ya tabbatarwa da zuciyarsa cewar: Allah ne kadai zai iya warkar da shi ba maganin ba kuma ba mai maganin ba, kuma yayi imanin cewa Allah ne ya dora masa kuma shi ne kaɗai ke da ikon yaye masa, sannan sai yadau hanyar sanadin waraka wanda shi ne neman magani kamar Ayoyin nan da za muyi bayaninsu da wasun su.

Waɗan nan Surori da kuma Ayoyin Alqur'ani da muka rubuto a lamba ta 18, su ne malamai suka ce ana iya karanta su ne wajan karya sihiri a cikin ruwa tare da ganyen magarya, a baiwa mai fama da matsalar yasha kuma yayi wanka da ruwan amma ba a toilet ba, a wajan da bai da najasa.

Kuma a rika karanta masa Ayoyin a cikin ruwa yana sha akai akai ko yazamar da ruwan shi ne ruwan shan sa a duk lokacin da yaji qishin ruwa, 

AMFANIN BAQIN MISKI WAJAN RABUWA DA JINNUL AASHIQ

Lallaikam Jinnul Aashiq yana da matukar naci da taurin kai saboda yana shiga ne ta hanyoyin mabanbanta kamar sihiri da wasun su, to amma idan har ana amfani da baqin miski da kuma wasu waɗanda za mu zayyana a nan gaba insha ALLAHu za a samu dacewa matuƙar anbi wasu qa'idojin da za'a bi domin tafiya tare wajan taimakawa maganin yayi tasiri yadda yakamata cikin iko da yardar Allah.

Yawancin mu bamu san baqin misk ba balle har musan amfaninsa wajan korar Jinnul Aashiq da ma wasu al'amura na dabam har ALLAH yakawo waraka a irin waɗan nan matsalolin, daga Fari sai Jan misk ne kawai muka sani.

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji yadda ake amfani da shi a jiki domin samun warakar cikin iko da yardar Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)