📚♦️ DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 26 ♦️📚▪️_*
*_✍️ Yusuf Lawal Yusuf_*
*_بَسْمِ اللهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ_*
قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ الْفَلَقِ(١) مِنْ شَرِّ مَا خَلَقَ (٢) وَمِنْ شَرِّ غَاسِقٍ إِذَا وَقَبَ (٣) وَمِنْ شَرِّ النَّفَّاثَاتِ فِي الْعُقَدِ (٤) وَمِنْ شَرِّ حَاسِدٍ إِذَا حَسَدَ(٥) الفلق: ١-٥
1. Ka ce: "Ina neman tsari da Ubangijin asuba.
2." Daga sharrin abin da Ya halitta.
3. "Da kuma sharrin dare idan ya lulluɓe da duhu.
4." Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle.
5. " Da kuma sharrin mai hassada yayin da ya yi hassadar."
Suratul Falaƙ, aya ta: 1-5.
*_Tafsiri_*
Allah (Subhanahu Wata'ala) ya buɗe Surar da umartar Manzonsa (sallallahu alaihi wa sallama) da ya nemi tsari da kariyar Ubangijin asuba daga sharrin duk wani mahaluƙi mai cutarwa, mutum ne ko aljani da dabba. Ya kuma nemi tsarinsa daga sharrin duk wani abu da sharrinsa yake bayyana a cikin dare yayin da ya lulluɓe da duhunsa, kamar wasu miyagun dabbobi ko ƙwari ko ɓarayi. Ya kuma nemi tsari daga sharrin mata masu sihiri waɗanda suke tofi a cikin ƙulle-ƙullensu na sihiri. Ya kuma nemi tsarinsa daga duk wani mahassadi idan ya yi aiki da abin da hassadarsa je saƙa masa.
*_Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:_*
1. Gaskiyar sihiri da hanyar magance shi.
2. Yawancin masu niyyar aikata sharri suna fitowa ne da daddare domin ƙoƙarin ɓoye kansu.
3. Masu sihiri babban sharri ne a cikin al'umma, don haka Musulunci ya yi umarni da kashe su.
4. Hassada babbar cuta ce mai kama zuciya wadda take sa mutum ya riƙa fatan gushewar wata ni'ima daga ɗan'uwasa, don haka zai yi ta ƙoƙari don ganin ya cim na mummunan burinsa.
5. Surar ta ƙunshi neman tsari daga dukkan nau'o'in sharri baki ɗaya.
Tsakure Daga Cikin Littafin Fayyataccen Bayani Na Ma'anoni Da Shiriyar Alƙur'ani, Tafsirin Sheikh Dr. Muh'd Sani Umar Rijiyar Lemu.
*_Telegram:_* https://t.me/DDAMG
*_13th Rajab, 1442A.H (25/02/2021)._*