DUK TSUNTSUN DA YAJA RUWA... 1
Acikin wadannan kwanaki aduk inda ka leka na kafafen yada labarai zaka tarar labarin FYADE wa yan mata shine abunda suke tattaunawa akai, shine abunda masu sharhi suke sharhi akai, kusan hankalin kowa ya koma kan wannan masifar, me addu'ar neman tsari yanayi, mai tsinuwa yanayi, mai jaje yanayi kowa da kalan fuskar da yake kallon wannan masifar, amma mu zamu kalle abun ta fuskace ta Shari'a (musulunci), sai dai zamu takaita akan ambato dalilin faruwar hakan da kuma hanyar magance hakan.
🔸 MATA KU KUKA JAWOWA KANKU
wasu zasuga kamar wannan kalma tayi kaushi sosai, amma kuma gaskiya ce, Mata sune suka jawowa kansu duk wani bala'i dake riskarsu musamman ta wannan masifa ta fyade.
Allah madaukakin sarki yana cewa acikin Alqur'ani mai girma
يأيها النبي قل لأزواجك وبناتك ونساء المؤمنين يدنين عليهن من جلابيبهن ذلك أدنى أن يعرفن فلا يؤذين وكان الله غفورا رحيما. (سورة الأحزاب ٥٩)
Ma'ana "Ya kai Annabi ka gayawa matanka da ya'yanka da matan muminai dasu lullube jikinsu gabadaya, yin haka shi zaisa aganesu baza'a cutar dasu ba, lalle Allah ya kasance mai gafara ne kuma mai rahama".
Ibnul Jauzy Allah ya masa rahama yake cewa "Dalilin saukar wannan aya shine, fasikai yan iska sun kasance suna cutar da mata idan sun fita da dare, idan sunga mace tanada lullubi ta rufe jikinta sai suce wannar cikakkiyar ya' ce, idan kuma suka ganta ba lullube ta bayyanar da jikinta a waje sai suce wannan baiwa ce, sai su afka mata su mata fyade, sai Allah ya saukar da wannan aya".
زاد المسير ٦/٢٢.
Ya ke yar uwa ki duba tunfa alokacin da Alqurani yake sauka, lokacin da manzon Allah yake raye, zamanin da manzon Allah yake cewa yafi kowane zamani ana samun irin wadannan yan iskan mutanen da burinsu shine keta alfarmar ya' mace, tun awannan lokacin sai Allah ya baki kariya da hanyar da zakibi ki tsira daga sharrin wadannan miyagun shine kadai ki sitirte jikinki, ki boye surarki, ki kama mutuncinki, kibi karantarwar da Allah ya baki, wannan shine kadai wallahi abunda zai tseratar dake daga sharrin su. Amma matukar zaki cigaba da bayyana tsiraicinki kina shiga ta banza batare da kin rufe jikinki ba to ki shiryawa irin wannan barnar. Allah da kansa yace "wannan shine yafi kusa da aganesu baza'a cutar dasu ba". Rufe jikinki shi zaisa aganeki cewa ke ta Allah ce, baza'a miki kallon banza ba, baza'a dauka kema yar hanu bace (kamar yadda suke fada) bal ma su wadannan yan iskan su zasu baki kariya alokacin da wani zai nemi cimiki mutunci, (wallahi ni shaida ne hakan ya faru akan idona). Dan haka kiji tsoron Allah kibi karantarwar Allah da manzonsa sai ki tsira duniya da lahira.
#zaurenfisabilillah
Telegram:
https://t.me/Fisabilillaaah
Instagram:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/