FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN ZUL HIJJA 01



FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN*_
                       _*ZUL-HIJJA*_
                   

                   _*DARASI NA ƊAYA*_

    
    _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

_Watan *Zul-Hijjah* Ɗaya ne Daga Cikin Watannin Musulunci Guda Goma Sha Biyu (12). Kuma Ɗaya ne Daga Cikin Watanni Huɗu Masu Alfarma, Wanda Ubangiji Yayi Hani da Yin Yaƙi da Aikata Zalunci a Cikinsu. Ubangiji (ﷻ) Yana Cewa:_

*{إِنَّ عِدَّةَ الشُّهُورِ عِندَ اللَّهِ اثْنَا عَشَرَ شَهْرًا فِي كِتَابِ اللَّهِ يَوْمَ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ ۚ ذَٰلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ ۚ فَلَا تَظْلِمُوا فِيهِنَّ أَنفُسَكُمْ ۚ......}*
[سورة التوبة: ٣٦]

_*“Lallai Ne Ƙidãyayyun Watanni A Wurin Allah Watã Gõma Shã Biyu Ne A Cikin Littãfin Allah, A Rãnar Da Ya Halicci Sammai Da Ƙasa. Daga Cikinsu Akwai Guda Huɗu Mãsu Alfarma. Wannan Ne Addini Madaidaici; Sabõda Haka Kada Ku Zãlunci Kanku A Cikinsu......"*_

_Yana Daga Cikin Falala da Baiwa da *Allah (ﷻ)* Yayiwa Bayinsa, Sai ya Sanya Musu Wasu Abubuwa da Bayin Zasu Samu Garaɓasar Samun Lada mai tarin Yawa. Watan Ul-Hijjah Yana Daga Cikin Watannin da *Ubangiji (ﷻ)* Ya Sanya Waɗannan Garaɓasa a Kwanaki Goman Cikinsu. *Allah (ﷻ)* Yana Cewa a Cikin Littafinsa:_

*{وَالْفَجْرِ# وَلَيَالٍ عَشْرٍ}*
[الفجر: ١-٢]

_*“Ina Rantsuwa da Alfijr# Da Darare Guda Goma".*_
_[Fajr: 1-2]_

_*Ibn Abbas (ra)* Yana Cewa: “Kwanaki Goman da Ubangiji ya Faɗa a Wannan Surar Ana Nufin Goman Farko na Watan Zul-Hijjah. Saboda Hadisin da *Manzon Allah (ﷺ)* Yake Cewa:_

 عن ابن عباس ضي الله عنه قال : قال رسول الله صلي الله عليه وسلم: *"ما من أيام العمل الصالح أحب إلى الله فيهن من هذه الأيام“* قالوا: ولا الجهاد في سبيل الله ؟ قال: *"ولا الجهاد في سبيل الله ، إلا رجلا خرج بنفسه وماله ، ثم لم يرجع من ذلك بشيء“*
[رواه البخاري]

_An Karɓo Daga *Ibn Abbas (ra)* Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Babu Wani Yini da Ayyukan Alkhairi Sukafi Soyuwa a Wurin Allah a Cikinsu Sama da Waɗannan Kwanaki (Kwanaki Goman Farkon Zul-Hijjah)"*. Sai Sukace: Koda Jihadi Saboda Allah? Sai Yace: *“Koda Jihadi Saboda Allah, Sai Mutumin da ya Fita da Ransa da Dukiyarsa, Sannan Be Dawo da Ko Ɗaya Daga Cikinsu"*._
_[Bukhari Ya Ruwaitoshi]_

_*YA ALLAH KA BAMU IKON AIKATA AYYUKAN ALKHAIRI A WAƊANNAN KWANAKI MASU ALBARKA*_

_Ana Zan Dakata, Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba_

_✍🏼Sulyman Yahya_
*{Abu-Aysha Al-Maliky}*
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)