YAWAITA AZUMIN NAFILA A GOMAN FARKON NA WATAN ZUL-HIJJAH



YAWAITA AZUMIN NAFILA A GOMAN FARKON NA WATAN ZUL-HIJJAH
Azumi yana cikin mafi girma aiyukan Dha'a kuma yafi mafi yawan aiyuka falala saboda Allah ya jin gina azumi zuwa gare shi,yace Azumi nasane,ma'ana babu wanda ya san girman ladarsa.

Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Allah madaukakin sarki yana cewa;Duk aiyukan dan Adam nasane in banda Azumi,Azumi nawane kuma ni zan bada ladarsa)*
@ﻣﺘﻔﻖ ﻋﻠﻴﻪ. 

*Azumi kala biyune ake so mutun yayi a wadan anan kwanaki*

*A-Azumin ranar Arfa*
Yin azumin ranar Arfa yana da falala mai girma kuma sunnane na Manzon Allah SAW.

Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ya kasance yana yin Azumin *ranar Tara ga watan Zul-hijjah,da ranar Ashura da kwanaki ukku a kowane wata*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺻﺤﻴﺢ ﺳﻨﻦ ﺃﺑﻲ ﺩﺍﻭﺩ ﺑﺮﻗﻢ 2106

*Falalar Azumin ranar Arfa ga wanda baije aikin Hajji ba*

i-Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Yin Azumin ranar Arfa yana kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekara mai zuwa)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3805. 

ii-Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Duk wanda yayi Azumin ranar Arfa Allah ya gafarta masa zunubansa na shekara guda biyu,shekarar da ta gabata da wadda ta biyo bayanta)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 6335. 

iii-Manzon Allah SAW yana cewa;
*(Yin azumin ranar Arfa,ni ina fatan Allah zai kankare zunuban shekarar da ta gabata da shekarar da ta biyo bayanta...........)*
@ﺻﺤﻴﺢ ﺍﻟﺠﺎﻣﻊ ﺑﺮﻗﻢ 3853. 

*B-Yin Azumin kwanaki tara gaba daya tun daga farkon wata har zuwa ranar arfa*

Daga Hafsat ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ tana cewa;
"Abubuwa guda Hudu Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ baya barin aikata su,*Azumin ranar Ashura,da Azumin kwanaki tara na farkon zul-Hijjah da Azumi ukku akowane wata,da raka biyu bayan fitowar alfijir"*
@ﺭﻭﺍﻩ ﺃﺣﻤﺪ ﻭﺍﻟﻨﺴﺎﺋﻲ ﻭﺍﺑﻦ ﺣﺒﺎﻥ ﻭﺻﺤﺤﻪ 

Kuma sunnane yin Azumi kwanaki tara na farko watan,saboda Manzon Allah ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ,ya kwadaitar da mu cikin yawaita aiyukan alkhairi awannan kwanaki kuma Azumi yana cikin mafi aiyukan alkhairi.

Allah ne mafi sani

_*ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ.​​*
Post a Comment (0)