FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN ZUL HIJJA 02



_*FALALAR KWANAKI GOMAN FARKON WATAN*_
                        _*ZUL-HIJJA*_
                    

                  _*DARASI NA BIYU*_

  _Da Sunan *Allah* Mai *Rahma* Mai *Jinqai*_

_Kamar Yanda Mukayi Bayani a Baya, Watan Zul-Hijjah Yana Daga Cikin Watanni Masu Alfarma da Ubangiji Yayi Umurni da a kiyaye Waɗannan Alfarma Nasu, Sannan Yana Daga Cikin Mafiya Falala Daga Cikin Watannin Musulunci. Idan Ana Biye Damu Insha Allah Zamu Kawo Kaɗan Daga Cikin Falalar Wannan Wata Mai Alfarma kamaf Haka:_

_*1. WATA NE DA UBANGIJI YAYI RANTSUWA DASHI:* A Cikin Watan Zul-Hijjah Ne Ubangiji Yayi Rantsuwa da Wasu Kwanaki Daka Cikinsa Saboda Ƙima da Daraja da Allah Yayi ga Waɗannan Kwanaki. *Allah (ﷻ)* Yana Cewa a Cikin Littafinsa:_

*{وَالْفَجْرِ# وَلَيَالٍ عَشْرٍ}*
[الفجر:١-٢]

_*“Ina Rantsuwa da Alfijir# Da Kuma Darare Goma".*_
_[Fajr: 1-2]_

قال ابن كثير رحمه الله: *"المراد بها عشر ذي الحجة كما قالهه ابن عباس وابن الزبير ومجاهد وغيرهم“*

_Ibn Katir (rh) Yana Cewa: *“Abinda Ake Nufi da Darare Goma Sune Kwanaki Goman Zul-Hijjah. Kamar Yanda Ibn Abbas da Ibn Zubair da Mujahid da Wasunsu Suka Faɗi".*_

_*2. FIFIKON AIKATA AIKIN ALHERI A CIKINSU:* Ubangiji Ya Zaɓi Kwanaki Goman Farko Na Zul-Hijjah Ya Fifita Dukkan Wani Aiki Na Alkhairi a Cikinsu Akan Sauran Watanni. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

عن ابن عباس ضي الله عنه قال : قال رسول الله صلي الله عليه وسلم: *"ما من أيام العمل الصالح أحب إلى الله فيهن من هذه الأيام“* قالوا: ولا الجهاد في سبيل الله ؟ قال: *"ولا الجهاد في سبيل الله ، إلا رجلا خرج بنفسه وماله ، ثم لم يرجع من ذلك بشيء“*
[رواه البخاري]

_An Karɓo Daga Ibn Abbas (ra) Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Babu Wani Yini da Ayyukan Alkhairi Sukafi Soyuwa a Wurin Allah a Cikinsu Sama da Waɗannan Kwanaki (Kwanaki Goman Farkon Zul-Hijjah)".* Sai Sukace: Koda Jihadi Saboda Allah? Sai Yace: *“Koda Jihadi Saboda Allah, Sai Mutumin da ya Fita da Ransa da Dukiyarsa, Sannan Be Dawo da Ko Ɗaya Daga Cikinsu".*_
_[Bukhari Ya Ruwaitoshi]_

_*3. UMURNIN YAWAN AMBATON ALLAH A CIKINSA:* Saboda Fifitashi da Allah Yayi ne Na Ruɓanya Ladan Ayyukan Alherin da Akayi a Cikinsu ne, Ubangiji Yayi Umurni da Yawan AmbatonSa a Cikinsu *Allah (ﷻ)* Yana Cewa;_

*{وَيَذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ فِي أَيَّامٍ مَّعْلُومَاتٍ}*
[الحج: ٢٨]

_*“Kuma Su Ambãci Sunan Allah A Cikin 'Yan Kwãnuka Sanannu”.*_
_[Hajji: 28]_

*قال ابن عباس وابن كثير يعني: "أيام العشر".*

_Ibn Abbas Da Ibn Kathir Sunce Abinda Ake Nufi da Kwanaki Sanannu Sune Kwanaki Goman farkon Zul-Hijjah"._

_*4. SUNE MAFI GIRMAN KWANAKI KUMA MAFI SOYUWA A WURIN ALLAH:* Yana Daga Cikin Falalar Waɗannan Kwanaki, Kwanaki ne da Ubangiji Yake Alfahari Dasu Musamman Ranar Arfa. Sannan Kwanaki ne da Ubangiji Yafi Son su Sama da Sauran Kwanakin Shekara. Hadisi Ya Tabbata *Manzon Allah (ﷺ)* Yana Cewa:_

عن ابن عمر رضي الله عنهما قال: قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: *”مامن أيّام أعظم عند الله سبحانه ولا أحب إليه العمل فيهن من هذه الأيام العشر، فأكثروا فيهن من التهليل والتكبير والتحميد“*
(رواه الطبراني)

_An Karɓo Daga Ibn Umar (ra) Yace: *Manzon Allah (ﷺ)* Yace: *“Babu Wasu Kwanaki Mafiya Girma a Wurin Allah Maɗaukaki, Kuma Babu Kwanaki Mafiya Soyuwan Aikata Alkhairi a Cikinsu a Wurinsa Sama da Waɗannan Kwanaki. To Ku Yawaita HAILALA da KABBARA da HAMDALA a Cikinsu".*_
_[Ɗabarani Ya Ruwaitoshi]_

_*YA ALLAH KA BAMU IKON AIKATA AYYUKAN ALKHAIRI A WAƊANNAN KWANAKI MASU ALBARKA*_

_Ana Zan Dakata, Sai Mun Haɗu a Rubutu Na Gaba_

_✍🏼Sulyman Yahya_
*{Abu-Aysha Al-Maliky}*


*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)