FARFESA MAI HIKIMA



FARFESA MAI HIKIMA

Wasu daliban Jami'ane suka tafi Night club sukai abin nan da ake kira da TILL-DAWN. Kuma sun san suna da jarrabawa washe gari, gashi kuma basuyi karatu ba. Saboda haka suka shirya yiwa farfesa karya. Sai suka sanya kaya masu datti kuma suka bata jikinsu da bakin mai. Da suka je ofis din Farsesa sai suka ce masa jiya da daddare sunje bikin abokinsu a wani kauye mai nisan 100km, a kan hanyarsu ta dawowa sukai faci, shine suka turo motar sai yanzu suka dawom; saboda haka suna neman Farfesa yai musu afuwa su dan dawo hayyacinsu kafin su zana exam din. Farfesa da yaji haka sai ya tausaya masu yace suje nan da kwana uku su dawo.

Bayan kwana 3 suka dawo, farfesa yace dasu tun da dai wannan jarabawa ce ta musammman kowanne daya daga cikin su hudun nan za a sashi a aji daban-daban baza a hada suba. Dayake sun yi karatu sosai kuma sun shirya basu damuba sukace sun yarda..... Jarabawar dai tana da Jimillar maki 100 kuma ta kunshi tambayoyi Guda biyar. Amman da sharadin idan daya daga cikinsu ya amsa ba daidai ba to dukkan su hudun zasu samu zero mark.

Tambaya ta daya:
Rubuta sunan ka da lambarka...(20point)
Tambaya ta 2:
Ya sunan Ango da Amaryar da kuka je bikin su (30marks) 
Tambaya ta 3:
Wacce irin Mota kuke tukawa (20marks)
Tambaya ta 4:

Waye acikinku direban Motar (15point)
Tambaya ta 5:

Tayar wanne bangare ce tai facin? (15marks) 
In ka/ki na cikin su ya za ka/ki yi?...lol
Post a Comment (0)