MUNA RIGIMA DA MIJINA SABODA YANA KASHEWA BUDURWAR SA KUDI

*_MUNA RIGIMA DA MIJINA, SABODA YANA KASHEWA BUDURWARSA KUDI?_* *Tambaya:* Assalamu alaikum, Malam Ina da tambaya nice mijina zai kara aure, sai yace: zai biya ma yarinyan kudin makaranta, kuma zai barta ta cigaba kafin ya aureta, ni kuma sai nace ban yadda ba, saidai ya bari idan ya aureta sai yayi mata, shine muke rigima akai, dan Allah malam amun karinbayani konayi laifi ? *Amsa:* Wa'alaikum Assalamu, to 'yar'uwa a fahimtata ba ki da ikon da za ki hana shi, tun da dukiyarsa ce, kuma yana da iko ya kashe ta yadda yake so, mutukar bai sabawa sharia ba, ya kamata ki bambance tsakanin budurwa da matar aure, tabbas sharia ta wajabtawa namiji yin adalci a tsakanin matansa, saidai matar da yake nema, ta banbanta da matar aure, tun da ba ta shigo ba, daidai take da ragowar mutanan waje, wadanda mai gidanki zai iya yiwa alkairi idan yana da hali, da fatan Hajiya za ta fahimci wannan bayanin don ta daina rigima akan abin da ba ta da hakkı akai. Saidai ba'a so a wadata waje, idan gıda ba ta koshi ba, da fatan mai gidanki zai kula da wannan. Allah ne mafi Sani 3\3\2016 Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa. Gabatarwa:- Ãbûbäkår Êkâ. Ya kai dan uwa mai Albarka ka taya mu yada wannan karatu/sako zaka samu lada mai yawa, domin yada ilimi yana da daga cikin Abubuwan da suke kusan ta bawa ga Mahalicci. ______________________________________ » Zauren 🔑 *_MIFTAHUL ILMI_* 🔑 (WhatsApp). ‎Ga ma su sha'awar shiga Zauren MIFTAHUL ILMI a whatsApp sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu (07036073248) ta ‎whatsApp.
Post a Comment (0)