KAR KAYI SAKACI DA ADDU'A YAUCE RANAR ARAFAH



KAR KAYI SAKACI DA ADDU'A YAUCE RANAR ARAFAH

Annabi (s a w) yace mafificiyar addu'a itace addu'a ranar arafah kuma abunda Ni da sauran annabawa muke fadi a ranar shine *LA'ILAHA ILLALLAHU WAHDAHU LASHARIKALAHU LAHUL MULKU WALAHUL HAMD WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN QADIR,* ka yawaita maimaita wannan kalma a yau sannan kar kayi sakaci wajen rokon ubangiji dukkan abunda kake so na bukatarka don kuwa yau ranace ta amsa addu'a sosai daga mahaliccin bayi, ubangiji kabamu mai kyau a duniya ka bamu mai kyau a lahira, ubangiji ka amsa mana addu'oinmu da duk wanda ya nemi mu tayashi addu'a ya Allah.

 IBRAHEEM SULAIMAN GAMA
  9/12/1442-H
  19/7/2021-M
Post a Comment (0)