Labarin wani Sarki mai hikima



*QISSA📓📚📓*

Labarin wani Sarki mai hikima. 

    A zamanin da can akwai wani gari da suke za6ar sarki wanda zai mulkesu na tsawon shekara daya kacal, idan shekara tayi sai su dauki wannan sarkin su dorashi akan giwa sannan su zagaya dashi cikin gari don yayi ban kwana da jama'ar wannan gari.
     Bayan an gama zagayawa da wannan sarki sai azo a dorashi akan jirgin ruwa a kaishi wani jeji mai nisa da wannan gari a ajiyeshi, anan zai gama rayuwarsa har ya mutu su kuma sai su dawo su sake za6ar wani sarkin, wannan itace al'adar wannan gari.
     Wata rana bayan sun kai wani sarki wannan daji suna dawowa sai suka ga wani jirgin ruwa wanda yake dauke da wani saurayi da yayi hatsari har ya nutse a cikin ruwa.
      Da ganin haka sai suka ceto wannan saurayi sannan suka daukeshi suka kaishi garin su, sannan suka rokeshi akan yazama sarkin su bayan sun masa bayani akan wannan al'ada tasu.
      Da farko ya nuna baya son wannan sarauta amma daga baya sai ya amince ya amshi wannan sarauta.
     Bayan kwana uku da nadashi sai ya tambaye wazirin sa da cewa, "Shin zaku iya kaini wannan jeji da kuke kai sarakuna tun kafin watanni sha biyu su cika? Sai wannan waziri nashi yace, " Me zai hana? Sai kuwa suka daukeshi suka kaishi wannan daji sai wannan sarki yayi duba zuwa dajin yaga gawarwakin sarakuna da suka gabata a yashe akan kasa, sannan kuma wannan daji bashi da tsari don kayoyine da miyagun namun daji masu hatsarin gaske a ciki.
     Koda wannan sarki yaga haka sai nan da nan yayi umarni ga mayakansa da subi dukkan namun dajin su kashe, cikin dan kankanin lokaci suka karkashe wasu kuma suka gudu.
       Bayan da sarki ya dawo gida sai ya yasa aka tara masa katti majiya karfi har mutum dari, sai ya dauke su aiki akan suje su tsaftace masa wannan daji sannan su kawar da gawarwakin sarakunan da suka gabata da kuma na wadannan namun daji sannan su sassare bishiyoyin da suke dajin.
     Bayan sun samu watanni biyu sai suka tsaftace daji, sai sarki yayi umarni da a shuka kayan marmari sannan a sanya kananan dabbobi irin su agwagwi, kaji, shanu, tumaki, sai sarki yasa aka gina gida a wannan daji babba, kuma asa jiragen ruwa a gefen gidan.
      Don haka duk lokacin da hakimansa suka yi masa kyutar dukiya to sai yaje ya 6oye ta a wannan gida da aka gina masa a daji.
      Bayan cikarsa wata tara akan wannan mulki sai ya tara hakiman sa sannan yace musu, "Na sani a tsarinku kuna kai sarakunanku ne waccan jejin bayan watanni sha biyu to nidai a halin yanzu nake so a kaini tun yanzu.
    Da jin haka sai suka ce dashi, Bazai yiwuba domin hakan ya sa6awa al'adarsu don haka sai dai ya jira har bayan watanni uku sannan a kaishi.
     Hakan wannan sarki ya hakura har sai da yakai watanni sha biyu sannan suka daurashi akan wata katuwar giwa kuma suka sanya masa kayan alfarma masu tsada suka dinga tsagayawa dashi cikin gari mutane na masa ban kwana.
     Amma abin da yafi basu mamaki yadda wannan sarki yake daga musu hannu yana musu murmushi sa6anin wadancan da suke kuka, suka tambaye shi dalilinsa na yin murmurshi da murna, sai yace musu, " A lokacin da aka haifi jinjiri idan yazo duniya kuka yake yi wadanda ke kusa dashi suna murna, don haka kayi kokari kayi tanadi ta yadda zakabar duniyar kana farin ciki, su kuma wadanda ke gefen ka suna kuka, sarakunan da suka gabata sun shagaltu ne da jin dadi a lokacin mulkinsu ni kuma na shagaltu ne da gyran makomata har sai da wajen ya zama lambu ta yadda zanyi rayuwa ba tare da wata matsala ba.

_Da wannan nake jan hankulan mu da mu gaggauta gyara makomarmu don mu samu kyakkyawan karshe tun kafin lokaci ya kure domin duk wanda yake raye to wata dama ne da Allah ya bashi don ya gyara makomarsa._
     _Allah ya bamu dacewa da kyakkyawar karshe_


```Ga masu tambayoyi ko neman karin bayani sai a tuntu6emu akan wannan lambar mu kamar haka ``` 08137783797

✍🏻 *_Rubutawa_*
*_Ibraheem Khaleel_*

{08094000845} 
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)