MUMINI



MUMINI
Shi ne wanda ya ke tsoron Ubangiji Maɗaukakin Sarki da dukkanin gaɓoɓinshi kamar yanda wani Masani ya faɗa (( ابو الليث )) Abu Laisin " Alamomin Jin tsoron Ubangiji Maɗaukakin Sarki suna bayyana Daga Cikin gaɓoɓi guda bakwai ; 
1 - لسانه ( Harshen shi ) :- Na daga ƙauracewa yin ƙarya , zunɗe , Munafinci , Annamimanci da Gurɓataccen Zance .
 ya sanya Harshen shi wajen shagala da ambaton Ubangiji Maɗaukakin Sarki da Karatun Alƙur'ani da Neman Ilimin Addini .
2 -قلبه Zuciyar shi ;-Bai saka ƙiyayya ba ko kuma Hassada ga yan uwan shi ; Domin ita Hassada Tana janye kyakkyawan Aiki Kamar yanda Manzo Mai tsira da aminci ya faɗa (( Ita Hassada tana cinye kyakkyawan aiki kamar yanda wuta take cin karmami .
Ku sani ita Hassada tana daga cikin abubuwa masu girma da suke ruɗar da zuciya Kuma take kawo rashin ci gaba .
3 - نظره Ganin shi ;-Bai duba izuwa haramun Na daga abinci , abin sha da macen da ba tashi ba da Makamantan su , Ko wani abun duniya .
Sai dai ya kasance yana Juyar da ganin shi Izuwa bautar Ubangiji Bai dube izuwa abunda ba Halalin shi ba .
4- بطنه Cikin shi ;-Bai shigar da abunda Haram ne cikin shi Saboda Zunubi ne Maigirma .
5- يده Hannun shi ;-Bai saka Hannun shi Cikin Aikin Haramci Sai dai yana saka Hannun shi Cikin Aikin Biyayyar Ubangiji Maɗaukakin Sarki 
6- قدمه Ƙafar shi ;-Ba zai yi Tafiya Izuwa Saɓon Allah Ba , sai dai zai yi Tafiya Izuwa Biyayya Ga Allah da Koyi da Sahabbai da Manyan Bayin Allah .
7; طاعته Biyayyar shi ;-Zai sanya Biyayyar shi Wajen kaɗaita Allah shi kaɗai Ya ji tsoron yin Riya da Munafinci Idan ya Aikata Haka Yana daga cikin waɗanda Ubangiji Maɗaukakin Sarki ya ambace su a cikin alƙur'ani (( ان المتقين في جنات وعيون )) Suratul Hijr

Allah Yasa Mu Dace 

MS Kutama 
07044122219
Sat, 10 July 2021

Mukashifatul Qulub 
Imamul Gazali
Post a Comment (0)