Shin ko ana iya yin sujjadar ƙabli da ba'adi a sallar nafila?



*TAMBAYA.*❓
:
Shin ko ana iya yin sujjadar ƙabli da ba'adi a sallar nafila?
:
*AMSA*👇🏻
:
Mafi yawa daga cikin Malamai a da can da kuma a yanzu sun tafi ne akan cewa kamar yadda ake yin sujjadar rafkanuwa a cikin sallar farilla to haka nan ake iya yin ta a cikin sallar nafila babu wani bambanci. Kuma sun kafa hujja ne da wani Hadisi na Mαnzσn Allαh(ﷺ) da sukace hadisin ya game hukuncin yin ƙabli ko ba'adi a cikin kowacce irin sallah kamar yadda Mαnzσn Allαh(ﷺ) Yace:
:
"إذا نسي أحدكم فليسجد سجدتين" (رواه مسلم 402)
:
"وفي رواية قال"
:
"فإذا زاد الرجل أو نقص فليسجد سجدتين"
MA'ANA:
Idan ɗayanku yayi rafkanuwa (a cikin sallarsa) to yayi sujjada guda biyu (ƙabli/ba'adi)
:
A cikin wata ruwayar kuma yace: idan mutum yayi ƙari ko ragi (a cikin sallah) to yayi sujjada guda biyu (ƙabli/aa'adi)
:
Babban malamin nan mai suna (Ibn-Ƙudama) ya faɗa a cikin littafinsa (Al-mugni)
:
(Ibn Ƙudama) ya ke cewa:
:
Hukuncin sallar nafila dai dai ya ke da na sallar farilla a wajen sujjadar rafkanuwa kamar yadda Malamai suka faɗa, kuma ba mu san wani wanda ya saɓa akan hakan ba in banda wasu 'yan kaɗan daga cikin Malamai kamar irin su
(Imamu-Ƙatada) (إمام قتادة) da kuma
(Ibn-Sirin) (إبن سِرِين)

Domin kuwa shi (Ibn-Sirin) a fahimtarsa yana ganin ba za a yiwa sallar nafila sujjadar ƙabli ko ba'adi ba. To sai dai Malamai sukace wannan magana ta (Ibn-Sirin) ta saɓawa zahirin wancan Hadisi na Mαnzσn Allαh(ﷺ):
:
Sai dai kuma Mazhabin Malikiyya sun keɓance waɗansu abubuwa kamar guda (5) waɗanda suke ganin cewa idan an yi su a cikin sallar nafila to ba dole ba ne sai an yi sujjadar rafkanuwa a kansu ba, saɓanin inda ace a cikin sallar farilla ne a ka yi su, to idan itace sai an yi mu su sujjadar ƙabli ko ba'adi.
:
Dan haka magana mafi inganci itace ya halatta ayi sujjadar rafkanuwa a cikin dukkan nau'ika na sallolin nafila, haka nan ana iya yi a sallar Juma'a.

WALLAHU A'ALAM.
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)