Ramadaniyyat 1442H [9]
Dr. Muhd Sani Umar R/lemo
Rayuwar Sahabbai Babbar Shaida Ce A Kan Girman Martabar Annabi (ﷺ)
1. Alkur’ani cike yake da yabo da kyakkyawar shaida ga wadannan bayin Allah Sahabbai, ba don wani abu ba sai don a fito da girman Annabi (ﷺ) da matsayinsa da darajarsa a fili a idon duniya.
2. Hakanan an ga babban canji da ya bayyana a rayuwar wadannan sahabbai a sandiyar zamansu da Manzo Allah (ﷺ) da tasirantuwarsu da koyarwarsa. Domin duk wanda ya san tarihin Larabawa a jahiliyya, ya kuma ga yadda suka canja suka sake kamanni kamar ba su ba, to zai san cewa lalle addinin Musulunci addini ne mai tasirin gaske ga duk wata al’umma da za ta rungume shi ta yi aiki da koyarwarsa. Don haka rayuwar sahabban Annabi (ﷺ) babbar shaida ce a kan haka.
3. Yayin da muka yarda da haka, to a lokacin ne muka nuna wa duniya darajar wannan addinini namu da muke kiran mutanen duniya zuwa gare shi, da cewa shi addini ne wanda duk al'ummar da ta karbe shi, to zai yi gagarumin tasiri a cikinsu. Kuma dukkan wasu cututtuka da al’ummar take fama da su, da dukkan wasu wahalhalu a rayuwarta, to za su gushe, za a samu saukinsu. Shaida kuma a kan haka ita ce rayuwar sahabban Annabi (ﷺ) kafin su rungumi addinin Musulunci da kuma rayuwarsu bayan sun karbi Musulunci.
4. Saboda haka duk wani kokari na a ga an bata darajar sahabban Annabi (ﷺ), ko a nuna cewa wasu mutane ne da koyarwar Musulunci da tarbiyar da Annabi (ﷺ) ya yi musu ba ta yi wani tasiri a kansu ba, to wannan kokari ne na a ga an rushe Musuluncin daga tushensa. Domin duk sanda muka yarda da cewa, addini bai yi tasiri a zamanin wanda ake yi wa wahayi ba, watau Annabi (ﷺ), sannan bai yi tasiri ga mutanen da suka karbe shi daga bakin da ya fi kowane baki tsarki ba, kuma Alkur’ani bai yi tasiri ba a lokacin da yake sauka, a ke kuma karanta shi yana danyensa shataf, to zai yi matukar wahala a iya gamsar da wani cewa, Alkur’ani zai yi tasiri ga wata al’umma da za ta zo bayan shekara dubu da dari hudu (1,400) da saukarsa.
https://t.me/miftahul_ilmi