SHIN MUTUM ZAI IYA YIN ZAKKAR FIDDA KAI, DA ABINDA AKA BASHI KYAUTA KAMAR SHINKAFA?
*TAMBAYA*❓
_Assalamu alaikum warahmatullah malam Barka da warhaka ya ibada ya kokari, malam tambaya ta itace shin mutum zai iya yin zakkar fidda kai, da abinda aka bashi kyauta kamar shinkafa?
*AMSA*👇
_waalaikumussalamu Eh zai iya yi insha Allahu matukar dai 'kimar abincin takai ya fitar da zakkar fidda kan, kai koda shi wanda aka bawa zakkar fidda kan to idan an tara masa ita da yawa yadda shima zai iya fitarwa to shima An wajabta masa fitar da itan bawai zuwa zeyi ya tare ta a ma'ajiyar abincinsa ba a'a shima yayi zakkar fidda kan ga mabukata da abinda yayi ragowa daga abincin da aka tara masa Domin so ake yi musulmi ya kasance cikin farin ciki da walwala a wannan lokacin. Kuma wannan zai nuna maka kuskuren da wasu suke yi zaka samu an tarawa wani sadakar fidda kai wacce zai kai tsawon kwanaki yana ci Amma sai ya jibgeta a cikin gida bayan akwai sauran mabukata wadanda basu samu ba_
..
_Wallahu A'alam_
_ﺳﺒﺤﺎﻧﻚ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﻭﺑﺤﻤﺪﻙ, ﺃﺷﻬﺪ ﺃﻥ ﻻ ﺇﻟﻪ ﺇﻻ ﺃﻧﺖ، ﺃﺳﺘﻐﻔﺮﻙ ﻭﺃﺗﻮﺏ ﺇﻟﻴﻚ_
Zaku iya samu wannan group na Facebook da na telegram ta wannan hanyar
TELEGRAM👇🏻
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177