NAWA NE ADADIN KWANAKIN JININ BIKI ?



*NAWA NE ADADIN KWANAKIN JININ BIKI ?:*

*TAMBAYA*❓

Assalamu alaikum, malam dan Allah inada tambaya kwanaki nawane mafi yawan jinin biki?

*AMSA*👇:

Wa’alaykumussalam 
Imam Attirmizy yace: ” ma’abota ilimi daga sahabban manzon Allah S. A. W. da tabi’ai da wadan da suka zo bayan su duk sun hadu akan cewa mai biÆ™i zata aje sallah ne har tsawon kwana Ar’ba’in, saifa inta ga tsalki kafin cikar kwana arba’in sai tayi wanka ta cigaba da sallah koda jini ya dawo bayan arba’in toh dayawa cikin ma’abota ilimi sunce bazata bar sallah ba, wannan shine zancen mafi yawan masana fiqhu akan wannan fatawar ne Sufyanus sauri da Ibn mubarak da imam shafi’i da Imam Ahmad bin Hambal da Ishaq.” sunan Attirmizy 1/256
Malaman fatawa lajna sunce.. Kwana Arba’in shine cikar kwanakin jinin biki.

 Aduba fatawa lajnah 5/417.

Wallahu A’alam.
*MIFTAHUL ILMI*

ZaKu iya Bibiyar Mu a 
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml

Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi

WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248
Post a Comment (0)