TANA NEMAN MIJI NAGARI
https://chat.whatsapp.com/BsuVPYdzZY7C1Sv0lgoNES
*TAMBAYA*❓
Dan Allah a boye sunana... Ina bin pages dinka kuma inajin dadin yanda kake yiwa bayin Allah nasiha da kuma addu'oi.... Inada matsala kuma ina neman shawara... Ina da bukatar inyi aure sbd in raya sunnar manzon Allah s. A w amma kuma na kasance duk namijin da xai ce yana sona toh ba wanda xaixo da xancen aure bne hakan yasa kwata kwata bna kula kowa sbd da naga inda ka dosa se in daina kulaka.... Mutane sukan alakanta hakan da cewa aljani ya aureni tun mahaifiyata bata yarda har ya xamana abn ya fara damunta duk da bata fto ta nuna min ba.... Inada matsala na aljanu amma kuma shekara kusan takwas in an min rukiyya basa taba magana se dai su nuna alamu... Nakanyi mafarkin namiji amma kuma koda mun sadu a mafarki ban taba tashi naga wani abu ya ftomin ba... Tashin hankalina shine koda wasa bbu wanda ya taba xua wajena yanuna aure ne ya kawoshi ina cikin rudani ataimakamin da shawara da kuma addua... Ngd Allah ya saka da alkhairi amin
*AMSA*👇
Hakika kowacce irin damuwar da zata samu Mumini, to jarrabawa ce daga Ubangijinsa. Kuma kowacce jarrabawa tana cike da Kalu-bale (challenges) wadanda sai ka kiyayesu sannan ka samu cin jarrabawar.
Ki sani cewa rashin yin aurenki da wuri, Jarrabawa ce daga Allah. Su kuma wadannan Shaitanun Mazinatan samarin da suke zuwa gareki da wata manufa, su dinma jarrabawa ce daga Allah domin ya auna Qarfin Imaninki da kuma Taqwarki.
Kiji tsoron Allah kar ki nar shaitan ya rubza dake cikin ramin Hallaka mafi Muni in banda shirka babu laifin da yafi zina.
Ki sani cewa Mutukar kina ci gaba da Mafarkin saduwa, to bisa dukkan alamu Shaitanun Aljanun nan suma suna tare dake har yanzu baki gama warkewa ba. Don haka Ki ci gaba da zuwa wajen da ake yi miki rukiyyar su ci gaba da yi, kuma kina karbar magani.
Ki yawaita Qiyamullaili da sauran nafilfili da azumin tatawwu'I. Da karatun Alqur'ani da zikirin Allah safe da maraice, kuma ki rika yawaita Salatun Nabiyyi (saww) domin neman yayewar bakin ciki.
Allah yana cewa:
"Duk wanda yaji Tsoron Allah, to (Allah din) zai sanya masa Mafita, kuma zai azurtashi ta inda ba ya tsammani. Duk wanda ya dogara ga Allah, to Allah din zai isar masa".
(Suratut Talaq ayah ta 3).
Insha Allah Allah zai kawo miki Miji mai tsoron Allah. Kuma mai mutunci in dai kin kiyaye mutuncinki domin Allah.
Wallahu a'alam.
Ga ma su sha'awar shiga wannan group sai a turo da CIKAKKEN SUNA zuwa ga lambar mu ta WhatsApp
08087788208
08054836621
*_Group Admin: 👇_*
*MAL. HAMISU IBN YUSUF*