TONON SILILI



TONON SILILI

Wani magidancine yana zaune da matarsa suna fira sai tace bari na kawomaka abinci kaci, naga yanzu ka dawo daga kasuwa sai yace to Uwargida me aka dafa ne yau? Sai tace shinkafa da miya sai yace incedai ba agidan makwabcinmu kika siyo tumatur dinba ko? Sai tace kamar ka saniko can na siyo kenan yaya zanyi? Sai yace ina tsoron ko ya saka guba ne acikin tumatur din, saitace ai saida na fara baiwa karen gidannan tukunna kafin in kawomaka maigidana, sai yace to shikenan yafara cin abincin kenan sai "yar aikin gidan ta shigo tayi sallamah tace" Alhaji mai gadi yace na gayamaka Karen gidannan ya mutu, Nantake Alhaji ya karaya sai yacewa matar tasa kafin na mutu zan roki gafarar ki domin nayi miki laifi, Mun haifi yara biyu da "yar aikin gidannan. Sai matar tace nima Kayimini afuwa acikin yaranka guda shidda, Hudu na maigadi ne biyune kawai naka. Ana haka sai mai gadi ya shigo Alhaji wanine yayi sallamah yanzu koda na amsa sai yake gayamin cewa, abaka hakuri shine ya buge karennan da mota har ya mutu..

Tirkashi nan kuma assiri ya gama tonuwa. Wai Idan Kaine ko kece yaza ka/ki yi?
Post a Comment (0)