Allah Gwani | Ko ka san sau nawa zuciyarka ke harbawa kowace rana?
Zuciya ita ce famfon da ke harbawa domin buga jini zuwa dukan sassan jiki ba-dare-ba-rana domin ci gaban rayuwa. Rayuwa na tsayawa da tsayawar aikin zuciya.
Kwatankwacin girman zuciyar mutum ya kai girman dunƙulallen hannun mutum. Kuma zuciya tana bugawa sau 60 — 100 duk minti ɗaya yayin hutu, wato yayin da ba aiki ko motsa jiki ake yi ba. Saboda adadin harbawar zuciya [cikin minti ɗaya] na ƙaruwa yayin atisaye ko motsa jiki.
A kowace rana kuwa, zuciya na harbawa kimanin sau dubu ɗari (100,000). Inda take buga jini da ya kai yawan galan dubu biyu a kowace rana. Har wa yau, zuciyar na buga jini zuwa jijiyoyin jinin da tsayinsu ya kai mil dubu sittin (60,000 miles) in da za a warware tsayinsu.
Zuciya, sannu da aiki!