DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 32



*▪️🔖📖 DAGA DAUSAYIN ALƘUR'ANI MAI GIRMA 32 📖🔖▪️*

*✍️ Yusuf Lawal Yusuf*

*بِسْمِ اللَّـهِ الرَّحْمَـٰنِ الرَّحِيمِ*

وَالْفَجْرِ *(١)* وَلَيالٍ عَشْرٍ *(٢)* وَالشَّفْعِ وَالْوَتْرِ *(٣)* وَاللّيْلِ إِذَا يَسْرِ *(٤)* هَلْ فِي ذَلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجْرٍ *(٥)* سورة الفجر ١-٥

*1.* Na rantse da alfijir.
*2.* Da kuma darare goma.
*3.* Da kuma abin da yake cika da kuma mara.
*4.* Da kuma dare lokacin da yake tafiya (cikin duhu)
*5.* Shin a game da waɗannan akwai rantsuwa mai gamsarwa ga mai hankali?

*Tafsiri:*
Allah Subhanahu Wata'ala ya buɗe Surar da rantsuwa da abubuwa biyar:

*Na ɗaya,* Allah Subhanahu Wata'ala ya rantse da lokacin alfijir, wanda shi ne ƙarshen dare, kuma farkon gabatowar yini.
*Na biyu,* ya rantse da darare goma, watau kwanaki goma na farkon watan Zulhijja, kamar yadda ya zo daga Abdullahi ɗan Abbas da Jabir ɗan Abdullahi da Abdullahi ɗan Zubair da Mujahid da Masruƙ [Dubi, Mausu'tut Tafsiril Ma'asur, juzu'i na 23, shafi na 182-184].
An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas radiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: "Babu wasu kwanaki da Allah Subhanahu Wata'ala ya fi son aiki na gari a cikinsu kamar kwanaki goma (na farkon Zulhijja)". Sai aka ce? "Ya Manzon Allah, ko da jihadi don Allah?" sai ya ce: "ko da jihadi don Allah, sai dai mutumin da ya fita jihadi don Allah da dukiyarsa da kansa, amma bai dawo da komai ba." watau ya ƙarar da dukiyarsa wajen taimakon addinin Allah ya kuma yi shahada a fagen daga. [Bukhari #969].
*Na uku,* Allah Subhanahu Wata'ala ya yi rantsuwa da abu mai ciks, watau abin da yake bibbiyu ko hurhuɗu ko shida-shida da sauransu.
*Na huɗu,* ya rantse da abin da yake mara ne, watau ɗaya ne ko uku ko biyar da sauransu.
Rantsuwa da cika da kuma mara, ta ƙunshi rantsuwa da komai cikin halittar Allah wanda yake cikin ɗayan waɗannan abubuwa biyu. Watau ko cika ne shi ko mara ne.
*Na biyar,* ya yi rantsuwa da dare idan ya zo ya wuce da duhunsa.

Allah Subhanahu Wata'ala ya yi rantsuwa da waɗannan abubuwa ne don ya tabbatar da cewa, lalle za a yi wa mutane sakayya a kan ayyukansu. Sannan Allah Subhanahu Wata'ala ya yi tambaya cewa, shin a cikin waɗannan abubuwa akwai wata rantsuwa mai gamsarwa irinta ga duk wani mai hankali? Lalle duk mai hankali zai gamsu da waɗannan rantse-rantse da Allah Subhanahu Wata'ala ya yi.

*Daga waɗannan ayoyi za mu fahimci abubuwa kamar haka:*

*1.* Allah Subhanahu Wata'ala yana rantsuwa da duk abin da ya ga dama daga cikin halittarsa. Bai halatta bawa ya yi rantsuwa da komai ba sai da Allah.
*2.* Duk abubuwan nan da Allah ya yi rantsuwa da su abubuwa ne masu tasiri da muhimmanci a rayuwar ɗan'adam, domin sun ƙunshi lokuta masu nuna gwanintar Allah Subhanahu Wata'ala wajen tsara halittarsa. Ya halicci lokacin alfijir wanda ya ƙunshi ƙarshen dare da mafarar yini. Ya kuma yi dare wanda ya ƙunshi duhu zalla, kuma duk waɗannan lokuta sun ƙunshi lokutan bautar Allah da ayyukan alheri kamar kwanaki goma na farkon watan Zulhijja.
*3.* Falalar kwanaki goma na farkon watan Zulhijja, waɗanda su ne kwanakin da suka fi dukkan kwanakin shekara falala in ban da dararen goman ƙarshe na watan Ramadana.

Tsakure Daga Cikin Littafin Fayyataccen Bayani Na Ma'anoni Da Shiriyar Alƙur'ani, Tafsirin Sheikh Dr. Muh'd Sani Umar Rijiyar Lemu.

*Telegram:* https://t.me/DDAMG

*28th Zhulqi'idah, 1442A.H (9/7/2021)*
Post a Comment (0)