AMBATON ALLAH ANA YINSA A BAKI NE TARE DA HALARTO ZUCIYA



AMBATON ALLAH ANA YINSA A BAKI NE TARE DA HALARTO ZUCIYA

🍃🌹   

  Allah madaukakin sarki yana cewa: "Kada kayi biyayya ga wanda muka shagaltar da zuciyarsa daga barin ambatonmu, ya kasance Mai bin son zuciyarsa , sai al'amuransa gaba daya suka zama israfi ne". Surah Alkahf 28.

Shaikh Uthaimeen Allah ya masa rahama yana cewa akarkashin tafsirin wannan ayar, "Lalle acikin wannan ayar akwai ishara akan muhimmancin halarto da zuciya yayin ambaton Allah. Domin lalle mutumin da yake ambaton Allah da harshensa kawai batare da zuciyarsa za'a dauke albarka daga cikin ayyukansa da lokutansa har yakasance gabadaya lamuransa hasarace agareshi, zaka sameshi yana bata lokaci Mai tsawo amma bazai samu komai ba, amma da ace al'amuransa tare suke da Allah da ya samu albarka acikin dukkan ayyukansa".

تفسير سورة الكهف ٦٢

#Zurenfisabilillah 

TELEGRAM:
https://t.me/Fisabilillaaah

FACEBOOK:
https://www.facebook.com/Fisabilillaaah/

INSTAGRAM:
https://www.instagram.com/zaurenfisabilillah/
Post a Comment (0)