Gomnatin Taliban bisa Qa'idar Ahlus Sunnati wal Jama'a
Duk wanda ya rike Akidar Ahlus Sunnati wal Jama'a ba zai zama mai bin son rai da tufka da warwara ba da iznin Allah.
Idan ba a manta ba, a lokacin da aka yi juyin Mulki a Misra, Sisi ya zama shugaban kasa, wasu kungiyoyi guda biyu sun kishiyanci juna a kan lamarin:
1- Kungiyar Salafiyyun (Madakhila) sun yarda da shugabancin Sisi, suka yi masa mubaya'a.
2- Kungiyar Ikhwan sun ki amincewa da shugabancin Sisi, sun dauke shi a matsayin mai juyin Mulki, wanda mulkinsa bai halasta ba.
To yanzu kuma sai Allah ya kawo mu wani lokaci da Taliban suka yi juyin Mulki a Afghanistan, sai wadannan kungiyoyi guda biyu suka yi canjin matsayar da kowannensu ya dauka a game da abin da ya faru a Misra, kungiyar farko ta karbi matsayar kungiya ta biyu, ta biyun ta karbi matsayar ta farko. Ga bayani kamar haka:
1- Kungiyar Salafiyyun (Madakhila) sun fito suna ta sukar Gomnatin Taliban da ta yi juyin Mulki, da nuna kin yarda da shugabancinsu.
2- Kungiyar Ikhwan su kuma sai nuna murna da amincewa suke yi da shugabancin Taliban mai juyin Mulki a Afghanistan. Duk da cewa; juyin Mulki suka yi, kamar yadda Sisi ya yi a Misra.
Amma shi Ahlus Sunna mai bin Akidar Salaf, ka'ida daya ce a wajensa, duk shugaban da ya yi juyin mulki, har ya yi galaba, har ya kafa Gomnati, to ya zama shugaban da ya wajaba a yi masa mubaya'a, a yi masa da'a, da haramcin tube bai'arsa daga wuya.
Imamu Shafi'iy ya ce:
"كل من غلب على الخلافة بالسيف حتى يسمى خليفة ويجمع الناس عليه - فهو خليفة".
مناقب الشافعي للبيهقي (1/ 448)
"Duk wanda ya yi galaba ya kwaci mulki da karfi, har ya zama shugaba, mutane suka bi shi, to shi ne shugaba".
Babban Malamin Malikiyya Ibnu Battal ya hakaito Ijma'i a kan haka inda ya ce:
"الفقهاء مجمعون على أن الإمام المتغلب طاعته لازمة، ما أقام الجمعات والجهاد، وأن طاعته خير من الخروج عليه؛ لما فى ذلك من حقن الدماء وتسكين الدهماء".
شرح صحيح البخارى لابن بطال (10/ 8) وانظر أيضا: (2/ 328)
"Malaman Fiqhu sun yi Ijma'i a kan cewa; shugaban da ya kwaci mulki da karfi ya yi galaba to yi masa da'a dole ne, matukar zai tsayar da Sallar Juma'a da Jihadi, kuma yi masa da'a shi ne alheri a kan yi masa tawaye, don idan an yi masa da'an to an tsare jinane, kuma an yi maganin wawaye".
Don haka ka'ida ce guda daya a wajen Ahlus Sunna, duk wanda ya kwaci mulki da karfi, kuma al'amarin mulki ya tabbata a hanunsa, to ya zama shugaban da ya wajaba kowa ya yi masa da'a.
A takaice; duk wanda ya yarda da Mulkin Sisi dole ya yarda da Mulkin Taliban. Wanda ya yarda da Mulkin Taliban dole ya yarda da Mulkin Sisi.
Saboda haka wannan shi yake nuna mana tufka da warwaran kungiyoyi biyu masu kishiyantar juna, da irin sabawarsu ga Mazhabar Salaf Ahlus Sunnati wal Jama'a.
# Dr, Aliyi Muhd Sani
Daga
*miftahul ilmi*
Facebook⇨https://www.facebook.com/pg/Miftahulilmi.ml
Telegram⇨https://t.me/miftahul_ilmi
WhatsApp⇨ https://wa.me/2347036073248