ME YAFI WANNAN DAƊI?




ME YAFI WANNAN DAƊI? 
-
"Har kullum ace kina da wani bagiren da kike ƙaro ilmi wanda zaki daɗa sanin hukunce-hukuncen da suke kanki da rayuwarki musamman ta aure, to haƙiƙa wannan ba ƙaramar nasara bace gareki" 
-
"Ace ki zamto ɗalibar ilmi, me fafutuka da dagewa a wajen neman ilmin addinin musulunci da na rayuwa babu dare babu rana, sannan kuma ace kin more kuma kinyi dace da samun miji nagari me addini wanda zai ke ƙarfafar ki wajen ganin kin daɗa bawa neman ilmin ki muhimmanci hatta a cikin rayuwar auren ku, babu shakka wannan abin gwanin sha'awa ne, tabbas za kiga rayuwar ki ta bambanta da ta sauran wasu matan da basu da wannan babban dacen irin naki"
-
"Babu macen da tafi munin zama abar tausayi irin wacce ita jahila ce, bata da tarbiyya, bata da batun zuwa neman ilmi a rayuwarta, sannan kuma bata yi dace da samun miji nagari me addini wanda zai ke taimaka mata wajen neman ilmin ba, wanda yake shima kansa jahilin ne marashin ilmin rayuwa balle na addini"
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Facebook page
https://mobile.facebook.com/Hausa-Islamic-Pictures-Quotes-304897013359792/?ref=opera_speed_dial_freefb
Post a Comment (0)