BABBAN ABIN TAKAICI A RAYUWA.
-
❝Mukan wayi gari mu manta da sha'anin ubangijinmu sai kuma mu rungumi sha'anin rayuwarmu wacce babu komai a cikinta sai tarin kusa-kuran yau da kullum masu yawan gaske❞
-
❝Kullum munfi bawa tafarkin da muke jin daɗin binsa muhimmanci, misali yanzu ga alƙur'ani mai girma yana cike da saƙonni waɗanda dasu ne zamu gina rayuwarmu, amma mun ƙaurace masa mun biyewa social media, ya ilahi anya muna son goben mu tayi mana kyawu kuwa?❞
-
❝Babban abin takaici ga rayuwar wasu daga cikin mu musulmai shine: mutum yasan idan ya wayi gari ya nufi inda wayarsa take ko computer, sai yaje ya buɗe ta domin ya duba saƙonnin cikin whatsApp ɗinsa ko facebook ɗinsa, kodai dukkanin wani channel da yake amfani dashi a social media ya ɓata lokacinsa akai, ya kuma wuni yana chatting marasa amfani ga lahirarsa, sai ya manta da buɗe alƙur'ani littafin Allah domin ya karanta shi, haƙiƙa wannan babbar fitinah ce a rayuwarmu❞
-
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss