HARAMCIN ZUWA WAJAN BOKA KO DAN DUBA
Wanene Boka??
*A larabci ana kiransa da ALKUHHAAN,boka shine Wanda ikirarin sanin gaibun abinda zai faru nan gaba kuma yake baima mutane labarin abubuwan gaibu wadanda bai faruba sai nan gaba,kamar yace wane zai ci zabe ko wane zai fadi,ko wane zai auri wance ko wani zai saki matarsa*.
Wanene Malamin Duba;
*Da larabci ana kiransa da ARRAF, wato mai duba ko bugon kasa,shine wanda ya baima mutane labarin gurin da wani abu nasu ya bata ko abinda aka sace masu yace yana waje kaza,daga cikin abubuwan mutane da suke bata,yana ikirarin sabin gaibun abun da ya faru*.
Boka da Mai Duba dukkan su kafuraine sun kafirta saboda ikirarinsu akan cewa sunyi tarayya da Allah acikin sanin gaibu bayan Allah yana fadar cewa;
*(Babu wanda ya san ghaibu sai Allah shi kadai)*.
Kuma saboda kayarda Allah cikin abinda Allah ya fadar cewa babu wanda ya san ghaisu sai shi kadai,amma su suna cewa sun sani
Allah yana cewa
*(قُلْ لَا يَعْلَمُ مَنْ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ الْغَيْبَ إِلَّا اللَّهُ ۚ وَمَا يَشْعُرُونَ أَيَّانَ يُبْعَثُونَ)*
Ma’ana;
(Kace babu wanda ya san ghaibu cikin sammai ko kassai sai Allah shi kadai….)
@النمل 65]
*HARAMUNNE ZUWA WAJAN BOKA KO MAI YIN DUBA*
Daga Safiyyah bntu Abi Uzaid daga Daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ ورضي الله عنهن daga Manzon Allah ﷺ yace:
*(Wanda yaje wajan malamin duba ko Boka,sannan ya tambayesa wani abu kuma ya gaskatsa akansa,baza’a karbi sallolinsa ba na kwana arba’in)*
@رواه مسلم.
Awata riwayar yana cewa;
*(Duk wanda yaje wajan mai yin duba ko Boka,kuma ya gaskata abinda ya fada masa,hakika ya kafircewa abinda aka saukarwa da Manzon Allah SAW)*
@وفي مسند الإمام أحمد ،وأبو دَاوُدَ والحاكم والذهبي والألباني والترمذي وابن ماجه وغيرهم :
Daga daya daga cikin Matan Manzon Allah ﷺ tace;Manzon Allah ﷺ yace;
*(Wanda yaje wajan malamin duba sai ya tambaye shi wani abu,baza’a karbi sallarsa ba ta kwana arba’in)*
@أخرجه مسلم[2230].
Allah ne mafi sani
Allah ka karemu da imanin mu baki daya.
SUBSCRIBE TELEGRAM CHANNEL:👇
https://t.me/DailyHadithss