BAMBANCI {20}



BAMBANCI {20}

A qa'idar ilimin magani ana iya magance matsala ne da akasin abinda ita matsalar ke iya rayuwa da ita ko kuma abinda matsalar take kyama wanda ba ta so. Daga cikin abinda Jinnu ba sa son warinsa shi ne Misk musamman ma baqin misk, shi yasa masana suka ce ana iya amfani da shi Baqin Misk din ta hanya kamar haka:

1- A hada shi da wasu maya-mayan kamar su: Zaitun da Habbatus Saudah, sai a cakudasu wuri daya sai a karanta Ayoyin ruqya a ciki, ko duk abinda ya sauwaka daga cikin Alqur'ani sai a rika shafawa tun daga kirji har gwiwa, da kuma tsakiyar kai da ta ƙafafuwa da na hannuwa.

2- A sami shi baqin misk din shi kadai sai a rika shafa shi a al'aura musamman da daddare ( Amma shi ba za a karanta masa komai ba na Ayoyin Alqur'ani saboda za'a shafa shi ne a al'aura).

Insha ALLAHu cikin hikimar Allah matukar masu fama da Jinnul Aashiq suna shafa wadan nan abubuwan a ko da yaushe, kuma suna tsare imaninsu da mutuncin su wajan bin dokokin Allah daidai gwargwado, kuma a dogara ga Allah wajan neman waraka daga gare shi kadai, sai kaga an samu sauki sosai wata rana ma sai a nemi matsalar a rasa.

WASU ABUBUWAN DA JINNU BA SA SON WARIN SU

Irin abubuwan nan ana amfani da su ne wajan shafawa, ko ci, ko sha, ko kuma turarawa, kuma matuƙar mutum yana yawaita amfani da su akai akai insha ALLAHu zai rabu da jinnu ko wadanne iri ne kuwa da ikon Allah. Wadannan abubuwan su ne kamar haka:

1- Haltit

2- Raihaan (doddoya )

3- Za'afaraan

4- Albasa

5-Tafarnuwa

6- Qustul Hindi 

7- Habbatus saudah

8- Garafuni

9- Albabunaj ( Bado)...

Da sauran su...

Insha ALLAHu za muji bayaninsu a rubutu nagaba.
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)