BAMBANCI {27}


BAMBANCI {27}

Karin bayani game da amfani da Sana-Makkey kafin a sha hadin nan sai an bari ya huce kuma a karanta Alqur'ani aciki, duk Ayoyi ko Surorin da ka karanta insha ALLAHu za ka samu waraka Saboda shi Alqur'ani gaba dayansu waraka ne, amma za ka iya karanta wasu kebabbun ayoyi da Surorin da suke da alaqa da sihiri ko nuna girma da karfin Allah akan wanin Allah kamar yadda wasu malaman suka zayyano su, a rubutun baya mun lissafo su.

A rubutu mai lamba ta {26}, a lamba ta (1) sakin layi na 2 ayimin afuwa na yi kuskuren rubutu ko tuntuben alqalami wanda ban lura ba sai daga baya naji jama'a na ta neman karin bayani akan haka, abinda nake nufi a wurin shi ne: *"Bayan ta tafasa ita Sana-makkey din da kofin ruwa 1, sai a sauke kuma a tace a sanya zuma sai a karanta Ayoyin Alqur'ani, a barta ta huce tukunna kafin a sha sai a sha sau 1 a cikin sati kafin karin kumallo, a sati na 2 ma sai a tafasa ta da kofin ruwa 2 sai a sha, sati na 3 ma sai a tafasa da kofin ruwa 1 sai a sha, a sati na 4 Kuma sai a tafasa da kofin ruwa 2 sai a sha, idan an hada sun zama sau 4 kenan a cikin wata daya, a wani watan ma sai a kara yin haka".*

Hanyoyin warware sihiri da kuma magance matsalar shafar jinnu, ko kambun baka ko hassada da Kuma maita, wannan suna da yawa sosai saboda kowa da yadda Allah ya sanar da shi hakan, amma duk maganin da za kayi ko za ayi maka karka kuskura kayi wasu abubuwa kamar haka:

Karka kuskura ka wuce gona da iri, 

Karka kuskura kaje wajan Dan duba ko dan bori domin yayi maka magani,

Kar ka kuskura kayi maganin matsalar ka da abinda Allah da manzonSA suka haramta.

Kuma wajibi ne kasani cewa: Ba a warware sihiri da sihri, ba a fitar da jinnu da neman taimakon wasu jinnun yan uwansu.

Duk maganin da baka gane kansa ba kamata yayi ka bar batunsa.

Domin ba zaka taba rabuwa da matsalar ba matuƙar ba Allah kaɗai kasanya a gabanka ba, 

MASU RUQYA SUJI TSORON ALLAH....

Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji bayani akan ruqya da masu ruqya.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)