BAMBANCI {28}



BAMBANCI {28}

Rashin yin Ruqya da Ayoyin Alqur'ani da kuma wasu ingantattun Addu'o'in da suka tabbata a hadisan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kuma rashin bin qa'idar ita ruqyar da yadda ake yinta a shar'ance da wasu waɗanda basu san menene ruqyar ba, da kuma bokayen da suka shigo harkar gadan-gadan shiyasa duk al'amuran ruqya suka dagule, tayadda wasu bokayen ke buɗe gidan bokancinsu da sunan Islamic medicine ana fakewa da laqa sunan Islamic ana yin Shirka, saboda ganinsu idan suka sanya Islamic din nan za'afi yarda da su nan take.

Wasu masu yin ruqyar sam ba sa daraja Alqur'ani kuma ba sa baiwa Allah cancantarSA da ya cancanta da ita, suna karanta Alqur'ani yadda suka ga dama, sai su ma masu neman maganin suna da babban kuskure, da yawan su su dai kawai su samu lafiya suke bukata ta ko wanne irin hanya ce ba ruwan su da hanyar haramun ce wannan ko kuwa, a haka ne duk lamarin nan ya dagule mana, har yakai ALLAh yake fita sha'anin duk wani wanda ya rike wani abu a matsayin wanda zai ba shi waraka ba ALLAH ba, sai kaga ayi ta yin ruqya amma ba'a samun waraka, ba sauyi hasali ma wasu ciwonsu karuwa yake yi, saboda ba imani da Alqur'anin a zukatan mai maganin da ma wanda ake yiwa maganin, saboda shi Alqur'ani yana tasirine gwargwadon imanin da yake acikin zuciyar mai karanta shi.

Da zarar an kaucewa bin umarnin Allah da ManzonSA kuma aka rika aikata abubuwan da suka haramta da sunan neman magani to fa ba makawa ba za'a warke ba kuma an rika Shiga cikin damuwa kenan da wahalhalu iri-iri masu wuyar sha'ani, kamar yadda lamarin Shafar jinnu ya yawaita a tsakanin al'ummar mu ta Hausa fulani, abin akwai ban mamaki, tambaya ta anan shi ne: *Shin mu (Hausa/Fulani) kaɗai ne Muslmai a kasar nan da abinnan yafi yawa a tsakanin mu ne haka*?

A tawa fahimtar da kuma yadda naji daga bakunan wasu malamai da yan uwa ita ce: Abubuwan shirke-shirken da wasun mu ke yi a tsakanin mu ne yanzu ko kafirai ma ba sa yinsa, ga yawan zuwa wajan bokaye da yan duba da sauransu, shi yasa shedanu suka samu mazauni da masauki a tskanainmu saboda an dauke su da babban matsayi kuma ana aikata abinda suka ce a aikata saboda biyan bukata.


Allah yakara tsare mana imaninmu, Insha ALLAHu a rubutu nagaba za mu ci gaba.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. 

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu'ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu'aym)

Gmail:
rismawy86@gmail.com

WhatsApp :
+2348031542026

Telegram Channel:
https://t.me/Rismawymedicine
Post a Comment (0)