HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE YANA TSAMMANIN BUDURWA CE SAI YA BAYYANA MASA CEWA BA BUDURWAR BACE



HUKUNCIN WANDA YA AURI MACE YANA TSAMMANIN BUDURWA CE SAI YA BAYYANA MASA CEWA BA BUDURWAR BACE

*TAMBAYA*❓

idan Mutum ya auri Mace akan cewa Budurwa ce, bayan ya ke'be da ita sai ya tarar da ita ba a matsayin budurwa ba, to ya zai yi? 

*AMSA*👇

Hakan yana da dalilai, ta yuwu budurcin ya tafi ba ta dalilin aikata Zina ba, dan haka ya wajaba a kyautata mata zato matukar a zahiri mutuniyar kirki ce, kuma a zahiri tsayayya ce a addini, dole a kyautata mata zato saboda hakan, ko kuma ta taɓa aikata alfasha amma ta tuba kuma tayi nadama daga baya alheri ya bayyana gareta, to hakan bazai cutar dashi Mijin nata ba, kuma ta yuwu budurcin nata ya gushe ne saboda tsananin jinin Al'ada da take yi, domin lallai tsananin jinin Al'ada yana gusar da budurci kamar yadda Malamai suka ambata, Wani lokaci kuma budurci yana gushewa ta dalilin tsalle-tsalle daga wani waje zuwa wani wajen, Ko ta sauko daga saman wani waje zuwa 'kasa da 'karfi, budurci yakan gushe ta dalilin hakan, ba lallai bane sai ta hanyar aikata zina yake gushewa ba, a'a, idan Mace tayi ikirarin gushewar budurcinta ta wani dalilin da ba alfasha ba to babu matsala, ko kuma ta hanyar alfasha ne amma sai dai ta ambata cewa tilasta ta akayi ko fyaɗe aka yi mata , wannan ma bazai cutar dashi ba, idan har tayi jini ɗaya bayan faruwar lamarin (domin istibra'i), ko ta ambaci cewa ta tuba tayi nadama, kuma ta aikata hakan ne da rashin sani bisa kuskure sannan ta tuba tayi da na sani, hakan bazai cutar dashi ba, kuma bai kamata ya yaɗa hakan ba, kuma ya kamata ya rufa mata asiri, idan ya tabbatar da cewa tana da gaskiya kuma tsayayya ce kan addini, to ya zauna da ita ko ya saketa tare da rufa mata asiri Kada ya bayyana abun da zai kawo sharri da fitina"

Majmu'u fatawabni Baaz (20/286).

AMSAWA
Ash-Sheikh Abdul-Azeez Bin Baaz R.A

Ku kasance damu domin ilimintarwa da Fadakarwa da Tunatarwa a Sunnah.
KU BIYOMU A TELEGRAM:👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
KU BIYOMU A FACEBOOK👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
Post a Comment (0)