CIWO YAYIN YIN HAILA 2



https://sirassalafeey.wordpress.com/ciwo-yayin-yin-haila/

CIWO YAYIN YIN HAILA 2

Alhamdulilah, da farko yana da kyau mu sake sanin mecece haila? Kuma ya take? 

Haila tana nufin wani jini da ya ke fita daga gaban mace, a wani lokaci sannane, ba don wata cuta ba, kuma yana da bambamci tsakanin wata mace zuwa wata, kowace mace gwargwadon yadda Allah ya halicce ta, ko kuma yanayin wurin da take rayuwa.  

Kuma haila jini ne da ya ke zuba lokacin da mahaifa ta zubar da jini, wata sau É—aya a wata wata biyu, ya danganta dai. Wannan a taqaice kenan.

*_Menene ya ke haddasa ciwo mai raÉ—aÉ—i ga mace idan tana haila?_*

Wasu matan zaka ji sun ce maka da zaran lokacin hailan su ya gabato to sukan shiga cikin yayin raÉ—aÉ—i da ciwo, wanda mafi yawan ciwon ciwon mara ne, wanda ya kan kai ga mace ta kwanta rashin lafiya, ko ma idan ya tsananta sai anje asibiti. 

Wani bincike da na yi, da kuma mujallar lafiya da na duba, da kuma wani bincike da wata baiwar Allah ta turon, sun nuna cewa ana kiran ciwon a turance da *Dysmenorrhea* wanda ciwo ne da mata kanyi lokacin al'ada, a farkonta ko a karshenta kuma ya rabu zuwa kaso 2, akwai Primary da khma Secondary, wato matakin farko da mataki na biyu.

*Shi Primary Dysmenorrhea shine:* wanda yake faruwa sakamakon fitar wani sinadari da ake kira da *prostaglandin,* shi wannan kason ba shi da wata matsala, akasarin mata suna yinsa kusan kaso 70% cikin dari. Wannan kaso na farko ya kan dau kwatankwacin kwana 3 ne kacal ana yinsa, amma idan ya huce kwana 3 to ya shiga kaso na biyu kenan wato ya zama cuta.

*_Matan da suke yawan samun wannan ciwon na farko sun hada da:-_* 

-Matan da suka fara al'ada a kasa da shekaru 12.  

-Samu cewa dangin suna da tahirin suna yawan yin haila mai zafi. 

-Shan taba sigari ko shaye shaye. 

 -Zubar jini mai yawa lokacin haila

-Matan da suke sirara marasa kiba. 

-Rikicewar lokutan haila,

 -Macen da bata taba haihuwa ba. 

 *_Yadda ake magance wannan ciwo na farko_*

-Matan da suke yawan motsa jiki suna samun sauqin wannan ciwon. 

-Akwai ajin magani da ake kira NSAIDS, sune suke aiki wajen kawar da zugi, misalinsu sune: peroxicam, diclopenac, brustan N, Meloxicam, da sauransu. 

-Amfani pad mai dum. 

 -Yin wanka da ruwan dumi. 

 -Motsa jiki yau da kullun. 

 -Cin abinci mara nauyi, da abinci mai gina jiki. 

 -Yin yoga

-Shan magungunan kashe kumburi kamar ibuprofen kafin kwanakin al'adarki su zo. 

-Shan bitamin

-Rage yawan cin gishiri, da sukari don rage kumburin ciki. 

-Da sauransu da yawa. 

*✍️Abdullah A Abdullah Abou Khadeejatu Assalafeey*

15/01/1443
24/08/2021
Post a Comment (0)