*CIWON SO*
ruвutαwα
_Nasiru Kainuwa_
Har kullum abin da mawaƙa da marubuta ke gaya mana shi ne, ciwon so ba shi da magani. Haka ne ke sa wasu hallaka kan su domin sun sa a ransu matuƙar ba su sami abin da ransu ke so ba damuwa ba za ta bar su ba. Mawaƙa da marubuta sun gina mana danƙareren gida da tubalin:
In na rasa ki sai maƙabarta,
In ba ke ba zan rayu ba,
In ba kai ba sai rijiya,
Mun karanta a littattafai, mun saurara a waƙoƙi, mun kalla a fina-finai duk haka suke nuna mana cewa so na iya zama ajalin bil Adama, kuma mun yarda.
Kamata ya yi su nuna mana cewa:
A na warkewa daga ciwon so, Duk wacce ka rasa ko kika rasa za ki samu wanda ya fi shi.
Amma kash! sun ƙi ɗora mana wannan karatun. Sun bar mu so na azabtar da mu. Shi ya sa ma aka nusar da mu cewa kada mu yi soyayyar ƙure maleje haka ita ma ƙiyayyar, gudun kada wanda kake son wata rana ya zama maƙiyinka, ko masoyin naka ya zama maƙiyinka.
Duk wacce ka rasa ka tuna cewa da ba ka san ta ba, ka tuna cewa dama can Allah Ya rubuta ba matarka ba ce, ka tuna cewa wasu sun samu kansu a irin wannan halin da kake sun rungumi ƙaddarar, har ma sun sami soyayyar da ta fi wacce suka rasa. In har budurwarka za ta jure rashinka gare ta ta auri wani dan ba ka da halin aure, ya kamata kai ma ka tanƙwara zuciyarka ta haƙura da ita. Na taɓa yi wa so (soyayya) kuka, amma ba na jin zan ƙara. A yanzu dai ban ga wata soyayyar da zan yi asarar hawayena a kan ta ba.
Ke ma 'yar uwa duk sanda wani ya yaudare ki ko ya guje ki, ki sa a ranki dama can Allah Ya ƙadarta cewa ba mijinki ba ne, mahaifi ko mahaifiya ake rasawa a kasa maida kamarsu amma ba saurayi ba. Ku da kuke cewa namiji ba ɗan goyo ba ne, to menene abin damuwa dan ya guje ki? In kika yi haƙuri za ki sami wanda ya fi shi. Mawaƙa da marubuta ya kamata ku canja mana tunaninmu ta hanyar waƙoƙinku da rubutukanku, ku nuna mana cewa so ba cuta ba ne, ku nuna mana cewa rasa masoyi ko masoyiya ba shi ne ƙarshen rayuwa ba, kuma ba shi ne ƙarshen samun farin ciki ba a rayuwa.