MEYE ABU MAFI TSADA GAME DA MACE?



MEYE ABU MAFI TSADA GAME DA MACE??

Na jima ina Nazari dan in Gano "Me Annabi Musa yagani a Jikin Budurwar nan ta Madyana, Har ya yadda yai Shekara 10 Na Aiki Matsayin Sadakinta??"🤔

Sai Na samu Amsar ckn Faɗin Allah Ta'ala

تَمْشِي عَلَى اسْتِحْيَاءٍ

"(Budurwar) Tana tafiya cikin Kunya"

Allah(s.w.a) bai Siffanta mana Tsawonta Ko Dirin Halittar ta ba, A'a Sai Ya Siffanta ta Da Abu Mafi Tsada dake tare da ita, Shine KUNYA🤩

فَجَاءَتْهُ إِحْدَاهُمَا تَمْشِي عَلَى اسْتِحْيَاءٍ

Annabi Shuaibu(Mahaifinta) Ya Tarbiyantar Da ya'yansa akan Kunya, Sai Allah Ta'ala Ya Karrama shi ya kuma Karrama Ya'yansa🥰 Ya Kawo Musu Annabi matsayin siriki ya musu kiwon Dabbobi.

Kunyar Mace baya Tauye mata komai ckn Kamalarta, bal ma kara mata kyau yake da tsada, Ta yadda Matsiyaci bazai iya Taya Farashinta ba.

Dan haka Ƴar Uwatah kiji Tsoron Allah, Kunya da kamewa shine Siffofin Tsadarki wajen Mutanen kirki🤗

Hirarraki da maza a groups ko private wannan yana daga cikin alamun rashin kunya da rashin kamewa bal wannan dalili ne da yake kore nagartarki da tabbatar da rashin mutuncinki da rashin tarbiyyar gidanku

Mace ballagaza itace take washewa ko wane namiji baki 

Surutunki dasu nuna gazawar iyayenki ne wajen yimiki tarbiyya da bawa gidanku mummunar shaida

Duk abinda kikai a social media Zaki iya yin fiye dashi a zahiri domin magana itace tushen fitina

Fitar da Tsaraici Da Mai da kanki Araha(kowa na kulaki) bazai jawo miki kowa ba sai Ƙattin Banza(Ƴan killing time)
Post a Comment (0)